Yadda makarantu 79 a Misau ta Jihar Bauchi ke fuskantar ƙarancin malamai

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Aƙalla makarantu guda 79 ne dake cikin Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar Bauchi suke fuskantar matsanancin ƙarancin malamai masu koyarwa, inda kowacce ɗaya daga cikin waɗannan makarantu take da malami guda ɗaya tal dake karantar da dukkanin darussan ilimi a makarantar sa.

Wannan furuci mai ban tsoro da firgitarwa ya fito ne daga bakin Darakta mai kula da lamurran makarantu na Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Bauchi, Korijo Buba Umar a yayin zaman wani zauren tattaunawa na ‘yan jaridu na kwanaki biyu da Hukumar Kula da Asusun Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta shirya, da aka gudanar a garin Misau, da zummar shawo kan matsayar rashin halartar yara a makarantu dake cikin ƙananan hukumomin Misau da Alƙaleri na jihar.

Korijo Buba Umar yana kwatankwacin ne a zahirance yadda makarantu a cikin ƙaramar hukumar ta Misau, da ma na ɗaukacin cikin jihar baki ɗaya suke fama da matsalar ƙarancin malamai a ajijuwa.

Duk da la’akari da cewar, kusan kowace makaranta a taƙaice tana tutiya da malami guda ne, wannan matsayi ya yi matuƙar tauyewa yaran makaranta haƙƙinsu na samun wadataccen ilimi da ya dace da su na matakin firamare.

Umar ya ce: “A Ƙaramar Hukumar Misau, akwai makarantu guda 79 da kowacce take da malami ɗaya tal, kuma babu makarantar da ba ta da malami. Dukkan makarantun, kowacce tana da malami, illa dai ba su wadatar ba.”

Ya kuma yi ƙarin haske dangane da lamarin a makarantar ta Santaral Firamare ta garin Misau, inda malamai 24 suke karantar da yara 1, 726.

“Bisa ƙa’idar koyarwa da koya, kamata ya yi a ce akwai malami guda ga kowanne yara 45, tsarin ƙa’idar kenan da ya kasance gagara-badau a ƙasar Nijeriya.

“A wannan makaranta ta Santaral, tsarin shi ne malami ɗaya wa yara 72, lamarin da yake nuni da ƙarancin malamai a makarantu.”

Umar, sai ya nuna takaicinsa ga waɗansu makarantu dake cikin shiyyar, inda ake samun yara kimanin 150 zuwa 250 a aji guda a ƙarƙashin kulawar malami ɗaya, lamarin da yake ruruta wutar matsalar.

Hakazalika, Sakatare ko Baturen ilimi, kamar yadda ake kira, na hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Misau, Alh. Abdul ya yi la’akari da cewar dukkan waɗannan ƙalubaloli, makarantar ta santaral dake garin na Misau, ya ɗara bisa ga wasu makarantun dake cikin ƙaramar hukumar, wajen kusanci da bin ƙa’idojin koya da koyarwa.

Da yake nuna gamsuwar sa bisa halin da suka samu kansu a ciki, Abdul ya bayyana cewar, haka suke sarrafa gwargwadon malamai da suke da su, kuma tare da haɗin kan kwamitin gudanar wa (SBMC) ta makarantar ta santaral suke samun malamai masu taimaka wa koyarwa kyauta.

Dangane da yadda za a shawo kan matsalar ƙarancin malamai a makarantun jiha, Korijo Umar ya ce hukumar ilimi bai ɗaya ba ta da hurumin ɗaukar hayar sabbin malamai, illa lamarin yana wuyan wasu masu ƙoƙarin bunƙasa tsarin ilimi a cikin ƙaramar hukumar ta Misau, dama jiha baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *