Yadda matatar Fatakwal ta lamushe biliyan N39.4 a shekara ba tare da taɓuka komai ba

Daga AMINA YUSUF ALI

Duk da rashin tavuka komai a fannin tattalin arzikin ƙasa da matatar man fetur ɗin Nijeriya dake a garin Fatakwal take yi, a cikin watanni 12 kacal ta lamushe kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira biliyan 39.4.

Wannan matatar dai an ruwaito ta lamushe Naira 39,491,468,000 a cikin shekarar 2021 duk kuwa da ta kwashe shekaru ba tare da tace ko da ɗigon man fetur guda ba.

Waɗannan bayanan sun zo ne daga rahotannin bayanan kuɗin na Kamfanin Samar da Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) wanda hukumar PHRC ta gudanar a kan harkar mai na shekarar 2021. Kuma an saki bayanan ga jama’a ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata, 22 ga watan Oktoba, 2022.

Hakazalika, rahoton kuɗin ya bayyana cewa, matatar da ma ta lamushe Naira 31,463,168,000 a shekarar da ta gabaci 2021 (2020).

Kamfanin NNPCL ya ƙara da cewa, idan aka lura, kamfanin ya yi asarar Naira 9,758,817,000 a shekarar 2021 da kuma Naira 96,030,000 a 2020. Wannan yana nuna cewa, kadarorin kamfanin sun zama marasa amfanin komai kenan.

Domin asarar ta bayu ne sakamakon rashin tace ko da ɗigon mai da kamfanin bai yi ba a shekarar 202. Wannan ya sa kamfanin ma ya kasa mayar da kuɗinsa.

A dalilin rashin mayar da kuɗin ne kuma, kamfanin ya yi faɗuwar Naira biliyan 555.7 a shekarar 2021, sai 2020 kuma Naira biliyan 506.9. Kodayake, uwar kamfanin NNPC tana cigaba da tallafar kamfanin ta hanyar samar da dukkan kuɗin da zai cigaba da tafiya.

Sai dai kuma kafin wannan, shugaban zartarwar rukunin kamfanonin Injiniya Mele Kyari ya bayyana cewa, kamfanin ya samu riba har ta Naira biliyan 674 a shekarar 2021.

A cewar sa, wannan ribar da aka samu ce kawai daga abinda ya yi rara bayan an fitar da harajin Naira biliyan 287. A cewar sa ma wannan shi ne karon farko da aka samu wannan haraji mai yawa a cikin shekaru.