Yadda mawaƙa suka taya Aminu ALA murnar sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A sakamakon naɗin da aka yi wa fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar ALA a matsayin Sarkin Ɗiyan Gobir, a Masarautar Tsibirin Gobir da ke Jihar Maraɗi a Jamhuriyyar Nijar. Abokan sana’ar sa ta waƙa sun taya shi murna a wani gagarumin taro da aka shirya.

Taron, wanda aka shirya shi a ranar 12 ga Maris, 2022, a wajen taro na gidan Rediyon Premier da ke kan titin filin sukuwar dawakai a cikin garin Kano, ya samu halartar mawaƙa daga jihohi daban daban na ƙasar nan, in da suka shafe tsawon wuni guda suna bajekolin su don nishaɗantar da mahalarta taron.

Mawaƙiya Fati Nijar, ita ma ta halarci wajen, in da ta yi waƙoƙi na tsawon lokaci, wanda a cikin waƙar ta da ta fi jan hankalin mahalarta wajen, akwai waƙar ‘Carafke’ wadda waƙa ce mai cike da hikimomi da kuma sarrafa harshe, kuma ita waƙar daman asalin ta kamar mafarki ce, domin waƙa ce da tsananin shauƙin soyayya da mai taɓin hankali ya sa aka yi ta.

Bayan wannan, ta yi waƙoƙinta irin su ‘Girma Girma’ da kuma ‘Nijar Najeriya’ da sauran su.

Haka shi ma mawaƙi Baban Cinedu, baya ga waƙoƙin da ya gabatar a wajen, ya yi wasan barkwanci duk a ƙoƙarin sa na nishaɗantar da jama’a, kuma hakan ya sa ya samu yabo sosai daga wajen mahalarta taron.

Baya ga waɗannan, akwai mawaƙa masu yawa da suka yi waƙoƙi a wajen irin su; Sani Liya Liya, mai waƙar Sambisa, Sa’id Ja’afar Singa, Sagir Lalayyo Shalelen Waƙa, Ɗan Asharalle, El’Mu’az Birniwa, Fatima Khalil, Rabiu Birnin Gwari, Adam M Kirfi da dai sauran su.

A lokacin da yake jawabi a game da taron, Sarkin Ɗiyan Gobir, Aminu Ladan Abubakar Ala, ya yi godiya ga dukkan jama’ar da suka taru domin taya shi murna, musamman mawaƙa da suka bayar da gudunmawar su ta basira, in da yake cewa, “Mun haɗu a wannan waje ne don ɗan biki don taya murna, don haka aka shirya wannan taro don a ɗan yi nishaɗi da kaɗe-kaɗe da raye-raye na al’ada, saboda ita sarautar Sarkin Ɗiyan Gobir ma’anarta, kamar a ce minista ne na yaɗa labarai da kuma al’adu wanda ɓangaren abin da ya shafi al’adu da tarihi yana hannunsa, shi ya sa abin da suka shafi yawon buɗe idanu da kuma gargajiya duk suna ƙarƙashin ofishina a masarautar, don haka mutanen da suka zo taya mu murna daga wasu jihohi na ƙasar nan da ta Nijar domin a ce an gode kuma a tabbatar da wannan wakilci da aka bayar an bayar da shi a kan gaɓa.

“Don haka mu na tare da dukkan masoyanmu, su ma suna tare da mu kamar yadda a yanzu duniya ta tabbatar da hakan.”

Shi ma a nasa jawabin, fitaccen mawaƙi Yusuf Baban Cinedu, wanda ɗaya ne daga cikin abokai na kusa ga Aminu Ladan Abubakar, ya bayyana cewa, “wannan sarautar kamar mu aka yi wa, don haka Ina yi masa fatan Alheri, kuma Allah ya sa a gama lafiya, domin wannan nauyi ne babba da aka ɗora masa, kuma a matsayin mu na abokai na kusa, za mu yi duk mai yiwuwa, domin mu ga ya kai ga nasara, saboda nasarar sa ta mu ce, kuma gazawar sa ta mu ce, don haka ba za mu so mu gaza ba.”

Shi ma Shattiman Yamma na Zazzau Alhaji Ashir, ya bayyana cewa, “Wannan taron na Sarkin Iyan Gobir abu ne da mu ka ɗauke shi a matsayin na mu, na je Nijar ma, kuma cikin hukuncin Allah mun dawo lafiya, kuma abin da zan ce, shi daman mutum ne na mutane, kuma a yanzu da al’amarin sa ya taso kowa ya gani, don haka sai dai mu taya shi da addu’ar Allah ya cika masa muradin sa.”

Shi ma shugaban gamayyar ƙungiyar masu waƙa da yaren Turanci da Hausa, Malam Khalid Imam, cewa ya yi, “Babu shakka Aminu ALA kuma ɗan amanar Bichi, mutum ne da idan ya yi waƙa musamman ta sarauta za ka ji gargajiyar al’adar Bahaushe yake ƙoƙarin taskace wa da kuma adana abubuwa da suka shafi tarihi na Hausa, shi ya sa ban yi mamaki ba don sarakuna su na yi masa abin da a ke cewa yaba kyauta tukwaici.”

Shi kuwa Bulaman Lafiya, Alhaji Ibrahim Yayan Gida, cewa ya yi, “Daman shi Aminu ALA a cikin sarauta ya tashi, kaka da kakanni, saboda haka shawarar da za mu ba shi, sai dai mu ba shi a kan abin da ya sani, don haka mu na ba shi shawarar ya ci gaba da zama da jama’ar da ma wasu da za su zo nan gaba.”

Daga ƙarshe dai an karrama wasu mawaƙa da suka yi waƙoƙin da suka bayar da gudunmawa wajen kawo zaman lafiya a ƙasa.

Waɗanda aka karrama ɗin su ne; Fati Nijar, Adam M Kirfi, Fatima Khalil, Baban Cinedu da sauransu.