Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

A ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 ne ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta gudanar da taronta na ƙarshen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi.

Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Kannywoo TV da ke Tudun Yola a cikin birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana’antar shirya finafinan Hausa.

Babban abin da ya fi ba wa mahalarta taron sha’wa, ciki, har da wakilan kwamitin Amintattu da na kwamitin ayyuka na musamman da tsare-tsare, shi ne yadda Shugaban Ƙungiyar Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ɗauki lokaci wajen bayyana ayyukan ci gaba da mulkinsa ya samar a tsawon watanni 18 na zangonsa na biyu.

A cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Kakakin Ƙungiyar na Ƙasa, Al-Amin Ciroma, ya nuna cewa ko shakka babu, MOPPAN ta dawo cikin hayyacinta a ƙarƙashin mulkin Dr. Sarari.

Takardar ta nuna mahimman ayyukan da MOPPAN ta cimma a wannan zango na biyu, a matsayin babu wani shugaba a tarihin ƙungiyar da ya taɓa kawo mahimman ci gaba irin haka ga MOPPAN.

Wasu ma daga cikin shugabannin baya na ƙungiyar kamar Farfesa Umar Jibril, ya tabbatar da cewa mulkin Dr. Sarari ya ƙara buɗa mu su ƙwaƙwalwa, ganin yadda ya kawo ayyuka daban-daban da nasarori ga ƙungiyar.

Daga cikin ayyukan dai, har da gyara fasalin rajista da kuma biya kuɗaɗen ka’ida a kamfanin “CAC” mai kula da harkokin ƙungiyoyi na tsawon shekaru 18 da ba a yi ba, wanda hakan ta sa “CAC” ta cire MOPPAN cikin jerin ƙungiyoyi masu rajista a Nijeriya, amma a yanzu, MOPPAN ta dawo cikin tsari daidai da dokokin ƙungiyoyi masu zaman kansu na Nijeriya.

A ƙarƙashin mulkin Dr. Ahmad Sarari, MOPPAN ta ɗauki nauyin horas da da wasu daga cikin shugabanninta na jihohi a fannoni daban daban a lokacin taron horaswa (Masterclass) na bikin KILAF da ya gabata kwanan baya.

Har ila yau kuma, ƙungiya yar WIFFEN da tallafin ofishin Jakadancin ƙasar Faransa, wato French Emassy da haɗin guiwa da MOPPAN ta hanyar rattaba hannu a kan yarjejeniyar horas da mata matasa guda 11 harkar rubuta fim, faukar hoton fim, shirya fim, bada umarnin fim, sarrafa fitila da sauti a fim. Sun kamala an ba su shaida har su samar da fim ɗinsu na kansu.

Ƙungiyar MOPPAN ta cimma amincewar Ofishin sadarwa na Amurka dake Nigeiria ta bawa ‘yan ma’aikatar Kannywood horaswa ta musamman akan kasuwancin fim da sauran harkokin shirya fim mai inganci.

Bayan share shekaru da dama Sakatariyar MOPPAN ta ƙasa ba ta da office, Yanzu ƙungiyar samar da ofishin shelkwatarta na kasa No 6 Zoo Road, Royal Plaza, office mail amba 156.

Haka kuma, a ƙarƙashin mulkin Dr. Ahmad Muhammad Sarari ne MOPPAN ta sami damar jagorantar dukkanin ƙungiyoyin da ke yi wa masana’antar finafinai hidima ta ƙasa baki ɗaya, baya ga yunkurin tabbatar sake yi wa kundin tsarin mulkin ƙungiyar kwaskwarima domin tafiya da zamani, wanda a tsawon shekaru 20 ba a yi ba.

Mafi girman nasarar da mulkin Ahmad Muhammad Sarari ya samar wa MOPPAN ita ce samun damar gabatar da ƙungiyar ga fitacciya kuma babbar cibiyar tattara bayanai da bin diddigi na duniya Mai suna “PwC” inda a yanzu cibiyar ta amince za ta yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da MOPPAN wajen tattarawa da kuma dora kungiyar bisa turbar nasara a idanun duniya.

Cibiyar “PwC” ita ce da alhakin bin diddigi gami da ba wa manya ƙungiyoyi da hukumi shawarwarin ci gaba a duniya. “PwC” na da kyakkyawar hulɗa da Majalisar Dinkin Duniya, da ma’aikatun gwamnati da manyan bankuna da duniya, gami da wasu fitattun ƙungiyoyi masu zaman kansu na duniya.

A takaice dai Dr. Sarari ya bayyana mahimman ayyuka sama da 50 da nasarori da mulkinsa ya samar wa MOPPAN.

Kafin zaman na jiya Asabar, Kakakin ƙungiyar ya bayyana cewa Dr. Ahmad Sarari ya jagoranci tawagar shugabannin zuwa ga bude katafariyar sharkwata ta ƙungiyar, inda aka gudanar da kwarya-kwaryar bikin bude ofishin.

Haka zalika, bayan kammala taron, har ila yau, ya sake jagorantar shugabannin zuwa bude wani sabon ofishin ƙungiyar, reshen Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Malam Ado Ahmad Gidandabino, MON, ya samar.