Yadda mota ta ƙwace ta afka wa ɗalibai 30 a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Kimanin ɗaliban makarantar sakandare su sama da talatin ne suka tsinci kansu cikin wani mummunan yanayi bayan da wata mota ƙirar Siena ta saki hanya ta afaka musu a bakin titi a dai lokacin da suke ƙoƙarin komawa gida bayan tashi daga makaranta.

Wannan ibtila’in ya faru ne a jiya Litinin a Tudun Wada da ke yankin Uke cikin ƙaramar hukumar Karu, jihar Nasarawa da misalin ƙarfe biyu na rana.

Bayanan shaidu sun ce, lamarin ya auku ne sakamakon ƙwacewar da motar da lamarin ya shafa ta yi wa direbanta, inda nan take ta afka wa ɗaliban da suka yi dandazo a bakin titi, wasu na jiran abin hawa wasunsu kuma na neman sararin tallakawa bayan sun taso daga makaranta.

Tudun Wada, unguwa ce da ke bakin babbar hanyar Keffi zuwa Abuja, hanyar da ke fama da zirga-zirgar abubuwan kowane lokaci.

Manhaja ta gano cewa bayan aukuwar haɗarin, an kwashi wasu ɗalibai zuwa asibitin Uke da kuma asibitin tarayya ta FMC da ke Keffi don ba su kulawar da ta dace.

Haɗarin ya jikkata ɗaliban da lamarin ya shafa, inda wasunsu suka samu karaya da sauran munanan raunuka. Duk da dai babu bayanin haka a hukumance, amma dai da alama an samu hasarar rai sakamakon haɗarin.

Sa’inlin da wakilinmu ya kai ziyarar gani da ido a asibitin FMC da ke Keffi, a nan ya yi kiciɓis da shugaban ƙaramar hukumar Karu, Hon. James Thomas wanda ya je asibitin kan lamarin haɗarin ɗaliban.

Hon. Thomas ya shaida wa wakilinmu cewa lallai haɗarin ya munana, musamman ganin irin munanan raunakan da ɗaliban suka samu. Tare da cewa, za su yi bakin koƙarinsu wajen bada gudunmawar da ta dace don tabbatar da ɗaliban sun samu lafiya.

Wasu daga cikin ɗaliban da haɗarin ya rutsa da su

Suleiman B. Jibrin na ɗaya daga cikin waɗanda suka taimaka wajen jigilar ɗaliban zuwa asibiti, ya sanar da wakilinmu cewa haɗarin ya rutsa da wani ɗansa, tare da cewa a saninsa ɗalibai sama da talatin ne haɗarin ya rutsa da su.

Kawo yanzu dai an sallami wasu daga cikin ɗaliban waɗanda raunukansu ba su munana ba, yayin da sauran ɗaliban kuwa ana ci gaba da yi musu magani.

A hannu guda, iyayen ɗaliban da lamarin ya shafa sun nuna kaɗuwarsu kan halin da ‘ya’yansu suka tsinci kansu.