Yadda mota ta yi ajalin ɗaliban firamare 17 a Legas

Daga BASHIR ISAH

A Talatar da ta gabata aka samu aukuwar wani mummunan haɗari wanda ya laƙume rayukan ɗaliban makarantar Omole Primary School da ke yankin Ojodu a jihar Legas, su 17 ciki har da yara uku ‘yan gida ɗaya.

Faruwar wannan ibtila’in ya tada hankalin mazauna yankin gaya, lamarin da ya fusata ɗaliban sakandaren da ke kusa inda suka fito suka tare hanya sannan suka fafari babbar motar da ta aikata wannan ɗanyen aikin har zuwa yankin Ogba tare da banka mata wuta sannan aka kama direban.

An ga ɗaliban sakandaren cikin fushi sun mamaye duka hanyoyin da ke yankin suna hargowar nuna rashin jin daɗini game da haɗarin kafin daga bisani ‘yan sanda suka bayyana tare da harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa gangamin da aka haɗa a yankin.

MANHAJA ta gano cewa, ɗaliban sun cimma ajalinsu ne a kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun taso daga makaranta kuma a daidai lokacin da suke ƙoƙarin tsallake titi.

Wasu bayanan da ba a tantance ba sun nuna cewa, jami’an LASTMA ne suka biyo motar wanda a ƙoƙarin neman tsere musu ne haɗarin ya auku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *