Yadda muka kafa tarihin da ba a taɓa samu ba a NAHIMS – Shugaban ƙungiya

Daga SANI AHMAD GIWA

Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ma su Tattara Bayanai da Adanawa a Asibitoci ta Nijeriya (NAHIMS), Kwamared Jibril Salihi a Jawabin wurin taron ƙara wa juna sani na wuni biyu da ya gudana a Abuja, ya bayyana cewa, “mun shirya taron ne da sada zumunci da haɗin kai da son juna da ɗaga martabar ƙungiyar da ƙarfafa wa juna gwiwa akan sambuwar majalisar Zartarwa na ƙungiyar da aka zaɓa watannin da suka gabata.

Jibril ya ƙara da cewa, “al’umma su fahimci irin muhimmanci da sashin tattara bayanai da Adanawa a Asibitoci a Nijeriya.”
Manƴan baƙi ne daga sassan Nijeriya suka halarta, waɗanda ciki akwai Kwamared Biobelemoye J. Josiah shine mai ma saukin baƙi da Alhaji Babagana Mustapha Shugaban Majalisar zartarwa na Health Records Officers Registeration Board Of Nigeria (HRORBN), Lawal Aliyu Magaji shine wakilin Mataimakin shugaban Jami’ar ABU Zaria Farfesa Kabiru Bala da Yarima Timothy Ofoegbu ya wakilci Sanata Rochas Okorocha, da Alhaji Aminu Yakubu Wamabai shi ne wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau.

Taken taron na bana ‘Capacity Building and Leadership Retreat’, taron ya gudana a Ayuba Wabba House Sakatariyar ƙungiyar dukkan ma’aikatan asibiti ta Nijeriya a Babban birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, ranar uku da huɗu ga watan Nuwamba, inda wakilai daga duk kan shiyoyi na Nijeriya suka halarta.

Jibril ya miƙa saƙon godiya da ban gajiya ga ɗaukacin waɗanda suka zo da ba da tallafi don ganin an sami nasarar gudanar da taron cikin aminci aka gama lafiya. godiya ta musamman ga Kwamared Biobelemoye J. Josiah ‘National President Medical and Health Workers Union of Nigeria’ (MHWUN) da Mai Martaba Sarkin Zazzau da Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Kabir Bala da Sanata Rochas Okorocha da Alhaji Babagana Mustapha shugaban HRORBN ta Nijeriya da gidauniyar Neem ( Neem Foundation) da ’yan Jaridu da qungiyar matasan ’yan Jaridu ta Jihar Kaduna (KAYOJA) da Kwamared Hussaini Ahmed NVP (MHWUN). da Mallam Bello Hayatu MC.