Yadda muke ƙoƙarin sauya halayyar ’yan daba a Jos – Malam Nura Tela

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, yana ɗaya daga cikin manyan biranen arewacin Nijeriya, waɗanda suke fama da matsalar taɓarɓarewar tsaro, wanda ya shafi yadda ƙungiyoyin matasa ’yan daba suke ɗaukar makamai suna shiga unguwanni suna sare-saren kan-mai-uwa-da-wabi da ƙwacen wayoyi. Yawaitar wannan masifa ne ta zaburar da mutane irin su Malam Nura Alhassan Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Nura Tela, Shugaban Ƙungiyar ‘Jos Peace Vanguard’, tare da masu ra’ayi irin nasa suka tashi-tsaye, don ganin yaran da suke wannan aika-aika a garin, sun dawo kan hanya da samar da tsaro a cikin al’umma. Wanne ƙalubale irin wannan aikin sa-kai ke fuskanta? Wacce nasara aka samu? Kuma wanne tallafi waɗannan matasa ke buƙata? Za ku ji amsoshin waɗannan tambayoyi da wasunsu a zantawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, Abba Abubakar Yakubu, ya yi da Malam Alhassan. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu? 
ABDULLAHI: Salamu Alaikum. Sunana Nura Alhassan Abdullahi, wanda aka fi sani da Malam Nura Tela. Ni dai ɗan kasuwa ne da ke harkokin kasuwanci da sana’ar hannu ta ɗinki. Ina da shagunan ɗinki guda biyu da yara da ke ƙarƙashina, wasu na min aiki wasu kuma na koya. Tsawon lokacin da na kai ina wannan sana’a na koyar da yara da yawa da suka iya wannan aiki na ɗinki su ma kuma suka je suka buɗe nasu. Har yanzu kuma ni ne Shugaban Ƙungiyar Jos Peace Vanguard da ke aikin faɗakar da matasa ‘yan shaye-shaye da harkar daba, domin su daina munanan halayen su, su zama mutanen kirki. Ina da mata ɗaya da yara shida. 

Yaya aka yi ka samu kanka a wannan harka mai haɗari? 
Ni dai ga
waɗanda suka sanni ina gudanar da harkokin kasuwancina ne a ’Yan Tifa kusa da sabuwar kasuwar Jos, kuma ga duk wanda ya san cikin garin Jos ya san wannan waje ne da ya yi ƙaurin suna wajen harkar dabanci da matsalar ’yan shaye-shaye, zaman mu a wannan waje ya sa muna ganin abubuwan da ke faruwa, muna takaicin yadda yara matasa suke lalata rayuwar su da irin wannan harka marar kyau. Tun muna ganin abubuwan da ke faruwa muna kawar da kai har dai muka ga dole ne fa sai mun tashi tsaye mun taimakawa waɗannan matasa. Bayan mun yi la’akari da irin rashin jituwar da ke tsakanin su da jami’an ‘yan sanda da kuma ’yan banga. Alhamdulillahi, muna samun haɗin kan su, idan sun yi wani rashin hankali muka tsawatar musu suna saurarawa. A nan ne na fahimci cewa, za mu iya yin wani yunƙuri da za mu taimaki rayuwarsu. 

Ka na da wata ƙwarewa ne ko masaniya a harkar tsaro da ya sa ka jefa kan ka a wannan harka mai haɗari? 
Wallahi ban da wata masaniya a harkar tsaro, sai dai gogewa ta rayuwa ta yau da gobe. Ni dai abin da na sani shi ne ban iya ganin yaro yana yin ba daidai ba, in kawar da kai ban yi magana ba. Shi ya sa da na ga wannan al’amari na yaran nan yana neman ya ta’azara, saboda yadda suke yawan kai wa juna hare hare da yi wa mutane ƙwace a kan hanya, sai na je na nemi wani matashi ana ce masa Sadis Muhammad da ke Anguwar Rogo, daya daga cikin yankin da wannan abin ya fi muni. Muka zauna da shi na bayyana masa irin tunanin da nake da shi a raina, shi ma kuma ya nunar min da cewa abin nan yana ci masa tuwo a ƙwarya, ya rasa ya zai yi. To, da wannan bawan Allah muka fara shirya ganawar mu ta farko da shugabannin ƙungiyoyin matasan nan, a matakin anguwa anguwa. Kuma muka yi sa’a suka ba mu haɗin kai suka saurare mu. 

Mene ne alaƙar ka da jami’an tsaro da ƙungiyoyin ’yan banga, tun da wannan ba aiki ne da za ku yi ku kaɗai ba?
Tabbas wannan gaskiya ne. Sanin haɗarin da ke cikin wannan harka, da kuma gudun kaucewa shiga aikin wani ya sa ni da sauran abokan tafiya muka nemi haɗin kan jami’an tsaro da ‘yan banga da ke cikin unguwanni. Muna da kyakkyawar alaƙa tsakanin mu da su sosai, domin daga kan hedkwatar ‘yan sanda ta Jihar Filato, zuwa caji ofis na unguwanni, jami’an tsaron farin kaya, da sojoji da ke aikin samar da zaman lafiya a cikin gari, musamman ma dai nan Sector two, wato reshen rundunar jami’an tsaron haɗin gwiwa na biyu, inda muka samu wani soja mai kishi da ya riƙa tallafa mana, har ma ya taɓa sa wa mun haɗa masa wani zama da wasu daga cikin waɗannan matasa, kuma ya yi musu alƙawarin duk yaron da ya tuba ya daina harkar daba, zai samar masa aikin soja. Sai dai saboda yanayin aikin soja, bai jima sosai ba, aka yi masa canjin wajen aiki. 

Yaya ku ke samun ƙwarin gwiwar tunkarar waɗannan yara, bakwa tsoron su cutar da ku? 
Babu shakka akwai wannan. Amma cikin ikon Allah da muka fara sabawa da su sai tsoron ya fita. Mu burin mu dai mu ga yaran nan sun shiryu, sun koma makaranta ko wuraren sana’o’in su sun cigaba da rayuwa kamar kowa. Akwai wata rana da muka ziyarci babban jami’in ‘yan sanda na caji ofis ɗin Laranto, wanda ya roƙi mu taimaka masa game da wata daba ta hatsabiban yara da suka addabi hanyar Farar Gada da unguwar Sabon Layi, kuma sa yardar Allah haka muka yi bincike kan wajen da suke zama cikin tsohuwar tashar manyan motoci da ke kusa da kasuwar Farar Gada. Dama an ce mana da zarar mun je mu tambayi babban su ana ce da shi Kura, muna zuwa kuwa suka taso mana kamar za su cinye mu. Mu kuma muka ce musu ba jami’an tsaro ba ne, ga manufar mu, kuma muna son ganin babban su ne. A lokacin ba mu samu ganin sa ba, don ba ya nan amma daga baya mun koma mun same shi. Mun tattauna da shi kan manufofin mu da burin mu na son ganin mun taimakawa yaran nan sun samu sauyin rayuwa. A lokacin da muka same su ma kowannen su na ɗauke da makami a kan za su je ɗaukar fansa wata anguwa da aka tava musu ‘yan uwa. Amma cikin taimakon Allah muna musu magana, sai suka ajiye makaman suka kuma nuna mana jin daɗin abin da muka yi musu. 

Ko za ka gaya mana irin nasarorin da wannan ƙungiya ta ku ta samu a wannan taimako da ku ke yi? 
Alhamdulillahi, gaskiya mun samu nasarori masu yawa. Domin kuwa a duk lokacin da muka yi zama da waɗannan matasa dole ka nemi ka ji mai suke yi na dogaro da kai ko karatu. A lokacin mun taimakawa matasa da dama da muka samar wa wuraren koyon sana’o’i, ko abin sana’a, da kuma waɗanda muka mayar makaranta ta hanyar neman tallafin karatu daga wasu makarantu masu zaman kansu da ke cikin garin Jos. Mun godewa Allah, yanzu akwai waɗanda dama can suna da sana’ar amma saboda tasirin abokai ko matsalolin rashin samun goyon baya daga gida ko rashin zaman lafiyar iyaye, sai ka ga yaro ya samu kansa a wannan mummunar ɗabi’a, ya daina zuwa wajen sana’ar ya shiga shaye shaye. 

Waɗanne hanyoyi ko matakai ku ke bi wajen ganin kun kawo canji a rayuwar waɗannan matasa? 
To, lokaci zuwa lokaci muna shirya musu taron bita, inda muke gayyato jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA suna faɗakar da su kan illolin shaye-shaye, da masu koyar da dabarun kasuwanci, don ƙarfafa musu gwiwar tashi su nemi na kansu, wani lokaci ma har da malaman addini da za su riƙa yi musu nasihohi. Kuma a hakan ana sa’a ka ga wasu sun bayyana barin wannan harka tare da ɗaukar hanyar gyaran halaye da muhimmanci. A cikin su ne idan mun ga jajircewar mutum sai mu shigo da shi cikin ƙungiyarmu, don ya cigaba da taimaka mana, samun shawo kan sauran. Ka san an ce da ɗan gari a kan ci gari. Saboda su waɗannan matasa masu aikata halayen da ba su dace ɗin nan ba, ba sa shakkar kowa in ba shugabannin su ba. 

Kwanakin baya an samu matsalar sake dawowar wannan matsala ta sare-sare a unguwanni, inda har aka kashe wasu mutane, ciki har da wani malamin jami’a a Anguwar Rogo, yaya aka yi hakan ta faru?
Shi ma wannan rikici ne ya faru tsakanin ‘yan dabar ɓangaren ‘yan Kwaba da na tsallaken titin Madara, sakamakon kisan gillar da aka yi wani ɗan uwan wani ɗan dabar, wanda shi sam ma baya harkar daba, amma tsautsayi ya sa aka kashe shi. Allah ya saka wa kansilan Anguwar Rogo wanda shi ya yi ta kai kawo don ganin mun samu nasarar kwantar da wannan fitina, domin gudun kada a ce za a je ɗaukar fansa. Mun yi zama da su yaran daga ɓangarori daban-daban, har da masu anguwanni da manyan anguwa. Kuma sun amince babu sauran wata rigima, don har ta’aziyya muka je tare da su muka yi wa ‘yan uwan wanda aka kashe gaisuwa. To, abin da ya sa rikicin ya dawo ɗanye shi ne, wasu da suka qi yarda su shiga cikin zaman sasantawar da muka yi, su ne suka je suka ja zuga suka kai wannan harin a ɓangaren ‘yan kwaba da a ciki aka kashe wani malamin Jami’ar Tarayya da ke Gashua a Jihar Yobe. Bayan zama da muka yi da shugaban rundunar tsaro ta farin kaya da wasu manyan jami’an ‘yan sanda, an yi wasu kame kame da har yanzu ake kan bincike.

A ƙarshe, wanne jan hankali za ka yi ga iyaye da sauran masu faɗa a ji kan tarbiyyar yaransu da ke wannan harka?
In sha Allahu, muna sa ran nan da bayan Sallah ƙarama, za mu kira wani taron masu unguwanni da iyayen yara domin ƙara tunatar da su nauyin da ke kansu na yi wa yaransu tarbiyya da kula da duk wani motsi da suke yi na rayuwar su da abokai. Da kuma kira ga masu hannu da shuni da ke cikin unguwanni, game da tallafawa ilimin ’ya’yan makwabtan su, kada su riƙa ganin idan jifa ya wuce kaina da ’ya’yana, to ya faɗa kan kowa, wannan tunani ne marar kyau. Domin idan ɗan makwancin ka ya lalace kana ganin bai shafe ka ko yaranka ba wata rana a kan ka damuwar za ta sauka.

Wanne abu ne ka ke farin ciki da shi a wannan harka da ku ke yi?
Gaskiya babu abin da na fi jin daɗi irin na ga matashin da da aka san shi da mummunar rayuwa a ce yanzu ya tuba ya daina, ya zama mutumin kirki mai sana’a.

To, mun gode.
Ni ma na gode.