Yadda murabus ɗin ma’aikatan CBN ya janyo cece-kuce

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatan Babban Bankin Nijeriya (CBN) su 1,000 sun yi murabus na raɗin kansu a wani ɓangare na sake fasalin ayyukansa da nufin daidaita ayyuka da canji na dijital.

Yunƙurin, wanda aka yi don daidaita matakai da magance gurɓacewar wasu ayyuka, ya jawo ra’ayoyi iri-iri daga manazarta da ‘yan majalisa.

Bala Bello, mataimakin darakta a babban bankin na CBN, mai wakiltan gwamna Yemi Cardoso ne ya sanar da hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai.

An kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike a kan manyan ma’aikatan da suka yi murabus da kuma biyan diyyar Naira biliyan 50 ga ma’aikatan da suka bar aiki.

Da yake bayyana dalilinsa, Bello ya bayyana cewa, “Duniya gaba ɗaya tana gudanar da wani tsari na tantance ayyuka. Wannan yana haifar da dama da yawa amma kuma yana haifar da daidaito na ayyuka. Sake fasalin mu yana nufin daidaita ayyuka.”

Yunƙurin sake fasalin da Gwamna Yemi Cardoso ya jagoranta ya jawo yabo da suka.

Wani abin sha’awa shi ne, wasu ma’aikatan da ke barin aiki suna shirin kafa bankunan kansu, inda CBN ya yi alƙawarin bayar da tallafi. “A cikin waɗanda suka tafi, uku ko huɗu suna shirin kafa banki. Mun ba su tabbacin goyon bayanmu,” inji Bello.

A cewar Bello, an samar da tsarin ne tare da tuntuɓar shugabannin ƙungiyoyin bankin, tare da tabbatar da gaskiya da adalci.

Kwamitin majalisar wakilai, ƙarƙashin jagorancin Bello Kumo, na binciken shirin ne domin tabbatar da bin diddigin kuɗaɗen diyyar Naira biliyan 50 da aka biya.

Kumo ya tabbatar wa babban bankin CBN cewa batun na gaskiya ne, yana mai cewa, “aikinmu shi ne tabbatar da gaskiya da adalci a cikin wannan tsari.