Daga AISHA ASAS
A safiyar Lahadin da ta gaba ta ne, aka tashi da mummun labarin rashin ɗaya daga cikin ‘ya’yan masana’atar finafinai ta Kannywood, jarumin barkwanci kuma mawaƙi, Mahmud Nadanko, wanda ya haɗu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kano tare da ƙaninshi da kuma mai ɗakinsa da ke tare da jaririn ɗansu.
Wani abin tausayi da jan hankali ga mai rabo, wanda zai ƙara wa mai rabon shirya imani ya ƙara tabbatar da ba mai kashewa ko rayawa ba ya ga Allah shi ne, mai ɗakin tasa da ke tare da jinjirin ɗan mawaƙin, majiya mai ƙarfi ta bayyana mawalin ya rasu a hatsarin tare da ƙani da kuma mai ɗakinshi, sai dai yaron nasu ne kawai Allah bai kawo ƙarshen rayuwar tasa ba.
Kafin mutuwar sa, mawaƙin ya kasance jarumin barkwanci da yake sanya dariya a fuskar mutane da dama, daga baya ne ya koma harkar waƙa wadda ita kanta ta fi kama da barkwanci kasancewar kusan duk waƙoƙin da ya yi suna ɗauke da abin ban dariya, kamar waƙar ‘Baba Zai Daxa Aure’, ‘Olser’, ‘Za A Wa Mama Kishiya’, da sauransu.
Tuni mutane daga ciki da wajen Kannywood suka shiga alheni tare da jajanta mutuwar mawaƙin, wasu kuwa na bayyana kyawawan halayyar sa da irin yadda ya tava rayuwar su ta kyawawan hanyoyi.
Kasancewar mutuwar ta ba zato ba tsammani ya sanya ta zama mutuwa da ta taɓa zuciyar mutane musamman ma matasa waɗanda suka ji ta tamkar guduma da ta ƙwanƙwashi kansu, tana mai tunatar da su daga shagala da duniya da suka yi.
Da wannan suka shiga aiko da addu’ar rahma ga mawaƙin tare da fatan Allah Ya raya abinda ya bari, Ya kuma yafi nasu kura-kurai, Ya sa ƙarshen su ya yi kyau.