Yadda Nijeriya ta samu kanta akan gwiwa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun kafin hawan gwamnati mai ci ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Nijeriya ta samu kanta cikin ƙalubalen tsaro mafi girma a tarihin ƙasar nan. Tun daga lokacin da aka fara fuskantar matsalar masu ta da ƙayar baya a yankin Naija Delta, waɗanda suka ce suna yaƙi ne da matsalar gurɓacewar muhalli da kamfanonin da ke aikin haƙar man fetur a yankin suke haifarwa, zuwa ga rikicin addini da ƙabilanci a Arewa maso tsakiyar Nijeriya, da kuma kai wa ga bayyanar ‘yan ta’adda da ke alaƙanta kansu da addini, wato Boko Haram, masu da’awar jihadi da burin kafa shari’ar Musulunci a Arewacin Nijeriya.

Fantsamar rikicin ƙabilanci a jihohin tsakiyar Nijeriya irin su Filato, Nasarawa, Binuwai da Taraba shi ya hassala matsalar zaman doya da manja da aka daɗe ana samu a tsakanin manoma da makiyaya. A dalilin haka an samu asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi, da ƙaruwar gaba da ƙyamar juna tsakanin Fulani da ƙabilun tsakiyar Nijeriya, zuwa wani sashi na ɓangaren kudanci da gabashi. Wannan dambarwa ce ta kawo ga kafuwar gungun ‘yan bindiga masu fashi da satar mutane, waɗanda sau da dama aka fi alaƙanta su da Fulani makiyaya.

Daga jihohin tsakiyar Nijeriya zuwa yankin yammacin Arewa, irin waɗannan gungun ‘yan bindiga na nan suna hallaka jama’a da haifar da matsalar tsaro da lalata dukiyoyi da sanya rashin yarda a tsakanin ‘yan ƙasa. Ƙaruwar talauci da gurguncewar tattalin arziƙi da ƙaruwar ‘yan gudun hijira.

Daga jihohin Arewa maso Gabas, tarwatsewar babbar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta haifar da rabuwar ƙungiyar zuwa wasu qungiyoyi masu haɗari irin su ISWAP da ANSARU waɗanda duk da ƙoƙari da sadaukarwar da haɗin gwiwar rundunar sojojin Nijeriya ke ci gaba da yi na tarwatsa ayyukan su, da ƙwace garuruwan da suka mayar ƙarƙashin su, ba su daina barazana ga tsaron ƙasa ba.

Idan muka duba a ɓangaren kudancin ƙasar nan, musamman a yankin jihohin inyamurai da ke kudu maso yammacin ƙasar nan, an samu farfaɗowar ƙungiyar masu fafutukar sake kafa ƙasar Biyafara ta IPOB da ke barazanar kasancewar Nijeriya dunƙulalliyar ƙasa, da ƙaruwar wasu ƙananan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai suna iƙirarin ɓallewa daga ƙasar nan, don kafa ƙasar inyamurai zalla.

Rahotanni na baya bayan nan na nuni da cewa a yankin kudu maso yammacin Nijeriya akwai ƙungiyoyin ‘yan aware masu ɗauke da makamai fiye da goma, waɗanda ke ci gaba da haifar da tsoro da rashin zaman lafiya a zukatan ‘yan Nijeriya masu qaunar haɗin kai da lumana.

Waɗannan rigingimu da rashin tsaro su ne suka sa Nijeriya shiga cikin jerin ƙasashen duniya da ke yawan fama da ƙalubalen tsaro. A wani rahoto na baya bayan nan da aka fitar an bayyana cewa, Nijeriya ita ce ƙasa ta biyu bayan ƙasar Afghanistan da ake samun yawaitar mace macen mutane a dalilin rikice rikice masu nasaba da ta’addaci, ita ce kuma ta farko a nahiyar Afrika, yayin da Somaliya ke biye da ita a matsayin ta biyu. Gungun ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai na ci gaba da bayyana, da manufofi iri daban-daban waɗanda wasu za a iya warware su a siyasance ko ta hanyar amfani da tsare tsaren gwamnati.

A kowacce rana ta Allah sai an rasa rayukan farar hula ko jami’in tsaro. Ana danganta faruwar hakan ga rashin ɗaukar matakan da suka dace cikin gaggawa daga gwamnati da jami’an tsaro. Ƙarancin jami’an tsaro wajen iya tunkarar ta’addacin da ya addabi ƙasar nan daga vangarori daban-daban.

A yayin da ake daɗa tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, ‘yan siyasa da ƙungiyoyin kare muradun ɓangaranci da addini, da kanwa uwar gami baragurbin masu sharhi a kafafen watsa labarai, da ‘yan a fasa kowa ya rasa, na cigaba da amfani da zaurukan sada zumunta wajen yaɗa manufofin ƙiyayya da rabuwar kai a tsakanin ‘yan ƙasa, da nufin cimma mugun nufin su da son zuciyar su, don ganin ƙasar ba ta zauna lafiya ba, matuƙar ba a yi yadda suke so ba.

A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke murna da cigaban da ake samu a yaƙin da ake yi da Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas, rahotannin baya bayan nan da ke fitowa daga Jihar Naija na bayyana ɓullar wasu gungun ‘yan ta’adda da ake zargin suna da nasaba da aƙidojin Boko Haram a yankin Shiroro da maawabtan ƙauyuka, inda aka ce har sun kafa tutar jihadi a wuraren da suke iƙirarin kamawa, tare da kafa wasu dokoki da ke kishiyantar manufofin gwamnati. Duk kuwa da kasancewar rohoton ayyukan wannan ƙungiya ya daɗe yana fitowa ta kafafen watsa labarai. 

Tun da Nijeriya ta rungumi tsarin dimukraɗiyya ƙasar nan ke fuskantar irin waɗannan matsaloli, saboda munanan manufofi na ɓangaranci da ƙabilanci da wasu ‘yan siyasa da masu riƙe da madafun iko ke amfani da su, wanda suke ganin ta haka ne kaɗai za su iya samun ƙarfin faɗa a ji ko a dama da su a duk wata gwamnati da ta zo.

Yawan tarin makaman da jami’an yaƙi da fasaƙwauri ke kamawa a bakin iyakokin ƙasar nan, ana shigowa da su a ɓoye, ko wanda ake biyo da su ta ɓarauniyar hanya, amma jami’an tsaro su samu nasarar gano su, zai ɗaga hankalin duk wani ɗan Nijeriya mai kishin ƙasar nan, musamman idan ya yi la’akari da yadda harkokin tsaro ke daɗa lalacewa. Sai mutum ya fara tunanin ko dai wasu na shirin tada yaƙi a ƙasar ne! 

Masu nazarin harkokin tsaro na ci gaba da jan hankalin hukumomi game da tsananin buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan lamuran tsaro a ƙasar nan. Sanannen abu ne cewa, matsalolin da ake ciki sun yi wa jami’an tsaron da muke da su yawa, sannan gwamnati ba ta iya cimma yawan adadin sabbin jami’an tsaron da ta yi alƙawarin ɗauka duk shekara ba, sai an haɗa da ‘yan banga masu aikin sa kai da ba su da wata cikakkiyar ƙwarewa kuma ba a ba su wani tukwicin a zo a gani, da zai ƙarfafa musu gwiwa ko ya hana masu son zuciya a cikin su haɗa baki da ɓata gari. 

Har kawo yanzu dai an kasa cimma matsaya game da muhawarar da ake yi a Majalisar Ƙasa game da buqatar kafa rundunar ‘yan sanda mallakin jihohi da za su riƙa taimakawa wajen kula da ƙananan matsalolin tsaro na cikin gida da suka shafi fashi da makami, saɓani na ƙabilanci da rigingimun ‘yan tsagera da sauran su. Domin rage nauyin da ya yi wa sauran rundunonin tsaro na Gwamnatin Tarayya yawa. 

Lallai ne hukumomin gwamnati, rundunonin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, sadarwa da wayar da kan jama’a su duqufa sosai wajen ganin an samar da hanyoyi na inganta samar da bayanan sirri, wayar da kan ‘yan ƙasa game da muhimmancin kishin ƙasa, da daƙile yadda ake yaɗa labaran ƙarya da amfani da kafofin sadarwar zamani wajen angiza wutar rikici da savani a tsakanin ‘yan Nijeriya. 

Sannan yana da muhimmanci a riqa tabbatar wa ‘yan ƙasa irin hukuncin da ake yi wa waɗanda ake kamawa da hannu da laifukan cin amanar qasa, haɗin baki da ‘yan ta’adda da ma aikata ta’addacin kansa, domin ya zama izinina ga sauran ‘yan ƙasa masu mummunan nufi irin nasu. A yayin da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ke ganin muhimmancin voye bayanan sirri, ‘yan ƙasa na ganin hakan a matsayin wata gazawa da rufa rufa daga wajen gwamnati, kuma hakan na rage kima da darajar hukumomi, da ake yi wa kallon masu faɗa babu cikawa.

A farkon zuwan wannan gwamnati ‘yan Nijeriya sun yi burin ganin gwamnati ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu na fallasa masu cin amanar ƙasa da sace dukiyar talakawa, amma daga bisani sai zance ya canza, aka riƙa ƙumbiya-ƙumbiya da batun, har dai maganar ta bi ruwa. Ko da yake daga bisani wasu bayanan na fitowa jifa-jifa, amma ba yadda aka zata a farko gwamnati za ta fitar da jerin sunayen masu ci da gumin talakawa ba.

Yanzu ma da aka ji cewa, gwamnati na shirin tona asirin wasu ɓatagari da ke taimakawa ‘yan ta’adda ta hanyar ba su tallafin kuɗaɗen sayen makamai ko adana musu kuɗaɗe da tura su wani asusun ajiya na banki da idanun jami’an tsaro bai cika hawa kansa ba, ‘yan Nijeriya sun sa ran ganin a wannan karon gwamnati ta yi abin da suke tunanin shi ne daidai, kuma hakan zai daƙile yawaitar ayyukan ta’addaci a ƙasa. Nan ma dai daga bisani mun ji yadda turancin ya canja.
Ya kamata masu magana da yawun bakin gwamnati su riƙa tauna magana kafin su furta ta, domin wani lokaci suna sa gwamnati a halin tsaka mai wuya, kuma kimar shugabanni na daɗa zubewa, saboda zargin da za a riƙa yi musu na siyasantar da sha’anin tsaro ko rashin tsayar da magana ɗaya.

Idan muka koma kan maganarmu ta buƙatar ƙara yawan jami’an tsaro kuwa, ina ganin ya kamata gwamnati ta dubi shawarwarin da aka ce Sarkin Kano murabus, kuma masanin tattalin arziki, Sanusi Lamido Sanusi ya bayar a makonnin baya, inda ya bayyana buƙatar rage yawan kuɗaɗen da ake warewa ‘yan majalisun ƙasa, domin gudanar da wasu ayyukan cigaba ina ganin idan har an yi hakan za a iya juya akalar waɗannan kuɗaɗe a ɓangaren tsaro. Domin ɗaukar sabbin jami’an tsaro, samar da qarin makamai na zamani da horar da jami’ai kan sabbin dabarun yaƙi da ta’addanci, da inganta albashi da alawus alawus ɗin jami’ai da ke yaƙi a bakin daga.

Yadda Gwamnatin Tarayya ke kukan rashin kuɗaɗen tafiyar da gwamnati da muhimman ayyukan raya qasa, lallai ne a duba yadda kuɗaɗen da ake samu suke zirarewa ta hannun wasu ‘yan tsiraru da ke gwamnati da muƙarrabansu, ko ake almubazzarantar da su da sunan tafiyar da ayyuka, ko albashin masu riƙe da muqaman siyasa, don a rage wasu abubuwa da za su amfani wajen magance wasu daga cikin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan.