Yadda PDP ta lallasa APC a zaɓen cike gurbi a Kaduna

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

A jiya Asabar, 19 ga Yuni, 2021 aka gudanar da zaɓen cike gurbi a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kaduna ta sha kaye a zaɓen maye gurbi na ɗan Majalisar Dokokin Jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Alhaji Usman Baba na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin.

Shugaban hukumar zaɓen yankin mai suna Malam Mohammed Nuruddin Musa, shi ne ya faɗi sakamakon zaɓen ranar Asabar a sakatariyar Ƙaramar Hukumar da ke Zariya.

Malam Mohammed ya ce, “Usman Baba na jam’iyyar PDP ya lashe zaɓen da ƙuri’u 9,113, yayin da ya kayar da babban abokin karawar sa, Malam Musa Musa, na jam’iyyar APC, wanda ya samu muri’u 7, 404.”

Shugaban zaɓen ya ce “Alhaji Usman Baba na jam’iyyar PDP, shi ne ya lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari.”

Ya ƙara da cewa Malam Anas Abdullahi, na jam’iyyar ADC ya samu ƙuri’u 62, Chindo Ibrahim, na jam’iyyar ADP ya samu ƙuri’u 61, yayin da Musa Halilu na PRP ya samu ƙuri’u 304.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *