Yadda rikicin Aisha Buhari da ɗalibi Aminu ya ƙazance

Sakamakon wani rikici da ya ɓalle tsakanin uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, da wani ɗalibin jami’a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, mai suna Aminu Muhammad, Blueprint Manhaja ta tattaro wasu rahotanni na abubuwan da suka faru tun bayan fashewar zancen a ƙarshen mako. A taɓa a ji:

Kotu ta tura Aminu Muhammad kurkuku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ann gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Nijeriya, Aisha Buhari gaban kotu a ranar Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Lauyan ɗalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin ƙasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mista Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

”Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.’

”Akan haka muka buƙaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarrabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba.

Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar ‘yan sanda ta gabatar da buƙatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren buƙatar yau ko gobe,” inji CK Agu.

Tun da farko iyayen ɗalibi Aminu Muhammad sun faɗa wa BBC cewa za a gurfanar da ɗan nasu kotu a ranar Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman a Talata, kuma za a sake wani zaman  don duba buƙatar bada shi beli.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai ya ce ”yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari buƙatar bada shi beli.”

Tsare Aminu Muhammad wanda ɗalibi ne a Jami’ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da ƙura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ƙa’ida ba.

NANS ta yi barazanar yin zanga-zanga matuƙar ba a saki ɗalibin Jami’ar Dutse ba

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa NANS, reshen Jihar Jigawa ta buƙaci a sakar masu ɗan uwansu da jami’an tsaro suka kama a Jami’ar FUD da ke Dutse a Jihar Jigawa mai suna Aminu Adamu tun kafin su tsunduma gagarimin zanga-zanga a faɗin Nijeriya.  

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Ma’ajin ƙungiyar na ƙasa Bashir Suleiman wanda ya yi magana a madadin sauran ɗalibai na Nijeriya.  

An dai kama Aminu Adamu ne tun ranar takwas ga Nuwamba na wannan shekarar da muke ciki saboda rubutu da ya yi a shafinsa na Tuwita yana cewa matar shugaban ƙasa Aisha Buhari “Mama ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul”, lamarin da ya sa aka cafke shi zuwa birnin tarayya Abuja.  

Ma’ajin qungiyar ɗaliban ya dangantaka kama ɗalibin da jami’an tsaro suka yi baya bisa ƙa’ida kasancewar yaron ɗalibi ne da yake shekarun ƙarshe na karatunsa kuma yanzu haka yana daf da zana jarrabawar ƙarshe ta fita. 

Saboda haka suna buƙatar a sake shi domin ya samu ya zana jarrabawarsa ya dawo makaranta ya ci gaba da karatunsa. Amma matuƙar hakan bai samu ba a cewarsa za su gabatar da gagarumar zanga-zanga ta nuna rashin jin daɗinsu a faɗin Nijeriya a matsayin goyon bayansu ga Aminu Adamu Muhammed.

Naja’atu Mohammed ta yi kira da a kai Aisha Buhari kotu bisa cin zarafin ɗalibi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hajiya Naja’atu Mohammed, Kwamishiniya a Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta Ƙasa, ta buƙaci a gurfanar da uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari a gaban kuliya bisa laifin duka da kuma bayar da umarnin tsare wani ɗalibi, wanda ke shekarar ƙarshe a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu, da kuma tsohuwar hadimar ta kan kafafen sadarwa na zamani, Zainab Kazeem.

Jami’an ‘yan sandan farin kaya ne su ka kama Mohammed tare da azabtar da su saboda sukar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari a shafinsa na Tuwita, yayin da aka kama Kazeem ita kuma tare da lakaɗa mata duka bisa zargin ta da fallasa sirrin.

A wata hira da manema labarai suka yi da Naja’atu Mohammed ta caccaki uwargidan shugaban ƙasar kan abinda ta kira da ɗaukar doka a hannunta, inda ta yi kira ga jami’an tsaro da su kama ta tare da gurfanar da ita a gaban kuliya.

Ta ce dole ne dukkan ‘yan Nijeriya su yi Allah-wadai da matakin Aisha Buhari.

“Ba ta da ‘yancin yin hakan. Hasali ma ya kamata a tuhume ta da aikata hakan. Ta ɗauki doka a hannunta. Ta ɗauki matsayi da nauyin babban kwamanda.

“Ina ganin ya kamata ‘yan Nijeriya su tashi su ce a’a. Ba za mu ƙara yarda da wannan zalunci ba.

“Buhari ya bar wani givi a harkar mulki, shi ya sa kowane irin mutum ya samu damar shiga gwamnati.

“Ka ji fa, matar da ta ke ƙorafin cewa Mamman Daura ya karve ragamar mulkin mijinta, amma yanzu ta zama azzaluma. A bayyane ta ke cewa ba don Allah da kuma ‘yan qasa ta yi wannan maganar ba, sai dai son ran ta,” injita.

Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta nemi afuwar uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha kan tsare wani ɗalibin jami’ar tarayya da ke Dutse Jigawa, Aminu Mohammed da jami’an ’yan sanda suka yi.

Idan za a iya tunawa cewa, Hukumar SSS ta ce ta kama Aminu kan wani rubutu da ta wallafa a shafinsa na sada zumunta na yanar gizo da ta yi zargin vata sunan uwargidan shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari.

A cewar rahotanni, Aminu Adamu Muhammed ya yi a watan Yunin 2022, inda ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa ‘Aisha ta ƙara nauyi sosai bayan da ta taka rawar gani wajen wawushe dukiyar ƙasa yayin da talakawa ke sha wahala a ƙarƙashin mulkin mijinta’.

Muhammed ya wallafa cewa, “su mama an ci kuɗin talkawa an ƙoshi.”

NANS a cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun shugabanta, Usman Barambu, ta nemi afuwar a madadin ɗaliban Nijeriya ga uwargidan shugaban ƙasar, yayin da ya kuma yi kira da a saki Mohammed.

“Shugabannin NANS sun samu damuwa da labarin kama Aminu da ’yan sandan Nijeriya suka yi ba bisa ƙa’ida ba bisa umarnin Aisha Buhari.

Da samun labarin, ni, dangin Mohammed da abokanan arziki muka shiga aiki don gano inda Mohammed yake. Bayan kwanaki muna bincike, mun samu labarin cewa yana ofishin ’yan sanda da ke Wuse Zone 2. Na gana da Aminu a hannun ’yan sanda.

“An yi zargin cewa Mohammed a makonnin baya ya saka hoton Aisha Buhari a Tuwita tare da taken “Su mama an ci kuɗin talakawa an ƙoshi.”

“Kamar yadda al’adar ’yan ƙasa masu fusata ke da hanyoyin bayyana ra’ayi daban-daban a shafukan sada zumunta. A ranar 18 ga Nuwamba, 2022, ’yan sanda daga Abuja suka bi Aminu har zuwa Jami’ar Tarayya Dutse, suka ɗauke shi ba tare da wata gayyata ta rubutu ko ta baki ko sanar da shugabannin makarantar ko iyalansa ba,” inji Barambu.

Shugaban NANS ya yi zargin cewa an kai Aminu ne kai tsaye fadar shugaban ƙasa inda aka zarge shi da cin zarafinta sannna aka nakaɗa masa duka da wulaƙanta shi da cin mutuncinsa da ’yan sanda suka yi masa bisa umarnin Aisha Buhari, bayan haka an tsare shi ba bisa ƙa’ida ba a ofishin ’yan sanda da ke Wuse Zone II har zuwa yau.

Ya ce, “Ni tare da tawagar lauyoyinmu mun gana da Aminu a ofishin ’yan sanda inda ya tabbatar min da faruwar lamarin. Har ya zuwa yanzu, babu wata kotun da ta dace ta gurfanar da Aminu a gaban kuliya, ko kuma ’yan sanda suka bayar da belinsa.”

“Muna so a madadin ɗaukacin ɗaliban Nijeriya, mu miƙa uzurinmu ga uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari, kan matakin da Aminu ta ɗauka wanda ka iya jawo mata ciwo da danginta. Koyaya, a matsayinmu na shugabanni da masu riƙe da muƙaman gwamnati, dole ne mu yi watsi da wasu sukar idan muna son cigaba da yin abin da ya dace.

“Muna buƙatar ’yan sandan Nijeriya su yi cikakken bayani kan dalilin da ya sa za su je harabar makarantar su yi garkuwa da wani ɗalibi ba tare da bin ƙa’ida ba, sannan suka kai shi fadar shugaban ƙasa kai tsaye inda aka yi masa cin zarafi wanda ya keta haƙƙinsa na ɗan Adam,” sanarwar ta ce.

NANS ta ce, Aminu ya samu raunuka daban-daban kuma bai samu kulawar da ta dace ba. “Muna kira ga ’yan sanda a matsayin wani lamari na kishin ƙasa da gaggawa da su saki Aminu ba tare da wani sharaɗi ba ko kuma su shirya fuskantar ɗaliban Nijeriya.

“Duk da haka, muna kira ga ɗalibanmu da su yi taka-tsan-tsan tare da yin amfani da hankali wajen mu’amala da mutane musamman shugabanninmu. Su kula da abubuwan da suke wallafawa a shafukan sada zumunta.

Shugaban ya ƙara da cewa, “Muna son sanar da jama’a da su yi haƙuri yayin da muke jiran amsa da matakin da Sufeto Janar na ‘yan sanda zai yi a kan wata wasiƙa da ofishinmu ya aike masa tun da farko.”

Dole ne a saki ɗalibi Aminu – Amnesty

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce ya zama wajibi ga hukumomin Nijeriya su saki matashin nan da ake zargi da cin mutuncin uwargidar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari tare da yin watsi da duk zarge-zargen da ake yi masa.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an azabtar da matashin bayan kama shi.

Ta ce “babban abin kunya ne a ce hukumomin Nijeriya sun kama tare da azabtar da Aminu Adamu kawai saboda ya wallafa bayanai a shafin Tuwita wanda ya shafi uwargidar shugaban ƙasar.”

Bayanin ya ƙara da cewa wannan lamari karan-tsaye ne ga ‘yancin bil’adama.

Haka nan hukumar ta ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su mayar da hankali a kai shi ne tsarewar da aka yi wa matashin ba bisa ƙa’ida ba da kuma azabtar da shi da aka yi.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa kotu ta tura matashin mai suna Aminu gidan gyara hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin sa da cin mutuncin mai ɗakin shugaban ƙasa, A’isha Buhari a shafinsa na Tiwita.

Yadda ‘yan Nijeriya ke Allah-wadai da tasa ƙeyar Aminu zuwa kurkuku

Daga WAKILINMU

‘Yan Nijeriya na cigaba da yin Allah-wadai da tasa ƙeyar Aminu Muhammad wanda ake tuhuma da yin kalaman cin mutunci ga uwargidan Shugaban Nijeriya Aisha Buhari a shafinsa na Tiwita.

Jama’a dai da dama na ganin an wuce gona da iri wajen ɗaukar hukunci na lakaɗa masa duka kamar yadda ake zargi, inda kuma daga bisani kotu ta bada umurnin a tura shi gidan yarin Kuje kafin a cigaba da yi masa shari’a.

Tuni dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa da ƙasa a Najeriya irinsu Amnesty International su ka yi Allah wadai da matakin kama yaron tare da zargin an take masa haƙƙinsa na bil’adama.

Wani mai fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam, Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana cewa, “da farko dai laifin a Jigawa aka yi, sannan aka aika jami’an tsaro suka kama yaron suka je su ka kulle shi aka riƙa jibgarsa, wannan ya keta dokar ƙasa, ya keta dokar bil’adama.”

Haka shi ma wani matashi a Jihar Kebbi, Surajo Aminu, da yake nuna vacin ransa dangane da lamarin, ya bayyana cewa, “Aisha Buhari uwa ce ga ‘yan Nijeriya, kuma uwa ya kamata ta yi wa ‘ya’yanta faɗa ne da ja musu kunne. Ya kamata a ce ta yi haƙuri a matsayinta na babba, shi kuma yaro bai kyauta ba, girmama shugabanni wajibi a addinance da kuma dokar ƙasa.”

Bayanai na nuni da cewa uwar gidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ce ta bai wa jami’an tsaro umurnin ɗauko mata Aminu daga Jihar Jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta na zargin ta yi rub da ciki da kuɗin talakawa har ta yi ƙiba ta yi ɓul-ɓul a cewar Aminu, kalaman da ba su yi wa Aishar daɗi ba.

Sai dai a tsokacin da ta yi kan lamarin, Hajiya Naja’atu Muhammed wanda  kwamishiniya ce a hukumar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce ya kamata a kama uwar gidan shugaban ƙasar saboda ta keta doka.