Yadda rikicin Maitatsine ya faru

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Blueprint Manhaja ta yi nazari tare da tattaro bayanai daga masana dangane da labarin rikicin Maitatsine, inda za ta riqa kawo muku labarin sanka-sanka har na tsawon wasu makonni.

Maƙasudin rikicin maitatsine ya faru ne a ranar 11/12/1980, wato kusan a ce ya faru ne a unguwar Malafa, Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu Arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a ɓangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza.

A ɓangaren Malamai kuma, akwai irinsu Malam Umar Sani Fagge, da Malam Haido da su Malam Muktar Atamma, wanda duk a yankin unguwar Fagge su ke, da sauran manyan mutane. Haka zalika, to rikicin ya faro ne a gabas da unguwar Fagge daga ɓangaren kudu, yana da dangantaka da unguwar Ƙofar Wambai, wato K/Wambai.

Ita ce unguwar nan da ta shahara wurin sana’o’in gargajiya, kamar su Dukanci, Takalma da Jakankuna da Bel na ɗaurawa da sauran sana’oi iri-iri. Haka zalika, su ma na unguwar Fagge, suna da mashahuran mutane kamar irin su Bala Salisu da mashahuriyar qofar nan wanda aka fi sani da K/wambai, daga ɓangaren yamma unguwar malafa wanda a nan ne gidan Maitatsine ya ke ta yi iyaka da unguwar Koki, wato unguwar koki ita ce wadda wannan rikici na Maitatsine ya fi shafa wadda ko da a unguwar Malafa inda gidan maitatsine ya ke ba’a samu rasa rayuka da ƙone-ƙonen gidaje kamar yadda ya faru a unguwar Koki ba.

Ita unguwar Koki tana yamma da gidan Maitatsine, a nan unguwar Malafa Alhaji Nasiru Ahali ya ke farkon zamansa a nan unguwar sai da maitatsine ya kama iyalansa da matansa su huɗu da ’ya’yansa guda goma shabiyu har ya yanka ’ya’yansa guda biyu, daga ciki kuma ya yi garkuwa da matansa da sauran ahalinsa.

Haka zalika, a dai wannan unguwa ta Koki, sai da maitatsine ya kama ƙannen Alhaji Nasiru Ahali irinsu Alhaji Salisu Ahali, sannan a wannan lokacin ya yanka babban ɗan Alhaji Salisu Ahali, wato Umaru.

Bayan haka, ya kama Alhaji Yawale ya kuma kama iyalan Alhaji Yawale (17), inda ya yanka babban ɗan Alhaji Yawale, sannan ’ya’yanka shi bayan ’ya’yanka shi, ya samu iyalansa ya ce musu yau kun zama bayi na, na yanka mijinku, daga yau kun zama bayi na, saboda haka ko taso ku yi min godiya sakamakon yanka mijinku da na yi a taƙaice shi ya ɗauki kansa ne a matsayin shi Annabi ne.

A taƙaice dai duk labarin zai zo muku ta bakin matan da kansu a nan gaba. Sannan a nan unguwa ta Koki wacce maitatsine ya fi yi wa illa, a nan gidan Alhaji Almu yake, wanda ya kama iyalansa, da babban ɗansa mai suna Abubakar Yawale ya yanka shi. Sannan shi ma Alhaji Almun ya yanka shi, wanda duk labarin zai zo muku daga bakin wanda abin ya shafa. Bugu da ƙari, daga bayan unguwar ’yan awaki wato nan unguwar Malafa kenan, ita ce ta biyu wadda maitatsine ya yi wa illa, ita ma a cikinta akwai shahararren attajiri wato Alhaji Umaru Ta’ambo da sauran manyan mutane.

Maitatsine ya tayar da wannan fitina ne, sakamakon soyayya mai ƙarfi da ya ke nuna wa ɗansa Tijjani Kal’ana.

Dalilin da ya sa ake kiransa da suna Kal’ana shi ne, suna danganta Maitatsine da annabi kamar yadda ya umarce su, shi annabi ne, dalilin da ya sa suka yarda da annabtarsa, yana hawa kan buzu ya tashi ko ya doki hannayensa ya nuna musu daular duniya da ta lahira, nan Aljannace duk wanda ya bini zai shige ta.

Haka zalika, yana dukan hannayensa kuɗi su zubo ƙasa ya basu su je su kasha, to irin waɗannan tsafe-tsafen da ya ke yi sai suka ɗauka gaske ne, har suka yi imani da cewa shi Malam Marwa Maitatsine annabi ne, kuma a irin wannan tafiyar da ya ke yi yana da ɗansa Tijjani da sauran ’ya’yansa guda huɗu wanda ya haifi yara da yawa, amma dukkan su ba sa wuce shekara shida a duniya Allah ya ke ɗauke ransu, Tijjani shi ne ɗansa ɗaya, don hakan ya ke matuƙar sonsa sosai don haka ba abin da Kal’ana zai nema ya rasa, kuɗi ne ko suttura, sai wadda ya ga dama zai sa.

Hakan ta sa yaron ya fara lalacewa, shi ne bariki shaye-shayen giya nema mata da sauran kayan maye iri-iri. Maitatsine ya sangarta kal’ana, har ta kai ta kawo duk ɗan da aka sayawa keke sai Tijjani ya je ya samu babansa maitatsine ya ce an saya wa wane keke shi kuma maitatsine sai ya ce, ni kuma gobe babur zan saya maka, kuma ya saya masa babura iri-iri saboda gata da izzar kuɗi.

To ana wannan yanayi ne wata rana ya ɗebi abokansa, suka tafi yawon barikinsu da suka saba, sai suka tsokani wani kurma wanda aka fi sani da suna Sa’idu, sai wannan kurma ya buga masa wuqa a wuya, ganin haka suka ɗauko shi suka kawo shi gida inda Maitatsine ya ganshi hankalinsa ya tashi ya ce a kai shi asibitin Murtala. Bayan an kai shi bai jima ba Allah ya ɗauki ransa.

Tofa mutuwar Tijjani Kal’ana sai ta tunzura maitatsine ya ce, duk wanda ya ke wannan yanki na Malafa, Koki, Fagge, K/Wambai, Dukawa, sai ya ɗauki fansar ɗansa a kansu, sai ya ɗanɗanawa kowa ɗacin mutuwa.

Tofa yana wannan shirin afka wa al’umar unguwa, sai ya je wa’azi unguwar shahuci kusa da gidan Alhaji Ado Ɗandawaki da tawaga mai yawa, da suka kai mutum (2000) a bayansa, to ganin haka sai jama’a suka tsorata suka sanar da ’yan sanda, bayan ’yan sanda sun zo ne sai suka ga abin ya fi ƙarfin su sai suka fara buga musu barkonon tsohuwa, to fa daga nan ne a kai karan batta su kai kan ’yan sanda.

Akwai wani D.P.O na Kwalli a wancan lokacin, ana kiransa Muhammad Maikifa, wanda suka ƙona motarsa da ta wani Sufeton ’yan sanda ana ce masa Bukar Karim mutumin Lau a garin Jalingo. Sannan suka qona ’yan sanda guda huɗu, wanda bayan sun yi wannan bata-kashi ne suka dawo gida, suka biyo ta koki zuwa nan Malafa sai suka afka wa al’ummar unguwar, duk wanda suka gani sai sun sara ko su kashe. Daga baya sai suka kewaye unguwar duka, babu mai fita babu mai shiga. Suka zuba dakarunsu ko’ina.

Za mu cigaba a mako mai zuwa.