Yadda ruwan sama ya karya gadoji a Bauchi

Sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a jihar Bauchi ran Alhamis da ta gabata, hakan ya yi sanadiyyar karyewar babbar gadar da ta haɗa garin Bauchi da yankin ƙaramar hukumar Ningi a jihar.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna tazarar da ke tsakanin gadar da ainihin garin Bauchi kilomita 88 ne, kuma gadar ita ce mahaɗar hanyar Bauchi zuwa Ningi da kuma Bauchi zuwa Kano da Jigawa.

Kazalika, ruwan ya sake lalata wata gada a ƙauyen Nabordo a ƙaramar hukumar Toro, mai nisan kilomita 40 daga garin Bauchi, wanda hakan ya jefa masu nufin zuwa Jos da Abuja cikin wani mawuyacin hali.

Tuni dai jami’an Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya (FERMA) da ke yankin suka shiga aikin samar da mafita a yankunan da lamarin ya shafa don taimaka wa matafiya kafin a samu mafita mai ɗorewa.

Jami’an FERMA sun ce an dakatar da amfanin da gadojin da lamarin ya shafa na wani lokaci don gudun kada a samu akasi.

A hannu guda, Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Haya (RTEAN) reshen Jihar Bauchi, Abdullahi Mohammed, kira ya yi ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta wajen gyara gadojin don jama’a su ci gaba da zirga-zirgarsu yadda suka saba.