Yadda Sanata Babba Kaita ya lashe zaɓen fidda gwani na sanatan shiyyar Daura

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP ta ayyana Sanata Ahmed Babba Kaita a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen fidda gwani na shiyyar Daura a ƙarƙashin jam’iyyar.

Sanata Ahmed Babba Kaita wanda ya yi takarar ba tare da abokin hamayya ba, jam’iyyar ta ayyana shi bayan dukkanin masu kaɗa ƙuri’a wato daliget sun jefa ƙuri’ar amincewa da takarar tashi, a wani taro da ya gudana a Sakatariyar Jam’iyyar PDP ta shiyyar Daura.

Taron ya samu halartar wakilan Jam’iyyar PDP na Ƙasa, da na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ‘yan takarkaru na shiyyar Daura, gami da ɗan takarar Gwamnan a Jam’iyyar PDP Alhaji Salisu Yusuf Majigiri.

Haka zalika taron ya samu halartar ɗumbin magoya bayan Sanata Ahmed Babba Kaita wanda suka yi dafifi a ciki da wajen sakatariyar domin ƙara jaddada mubaya’a da goyon bayan su ga ɗan takarar Sanata Ahmed Babba Kaita.

Dayake jawabi jim kaɗan bayan Jam’iyyar PDP ta ayyana shi a matsayin ɗan takarar kujerar Sanata, Ahmed Babba Kaita ya gode wa masu zaɓe da suka ga ya cancanta suka zaɓe shi domin ya ƙara wakiltar su a Majalisar Dattijai ta Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyar PDP.

Ahmed Babba Kaita ya ce tun lokacin da ya dawo jam’iyyar yake ganin irin soyayya da goyon bayan al’umma da suke cigaba da nuna masa, sai ya sha alwashin cigaba da kawo ɗumbin ayyukan cigaba idan aka sake zaɓen shi a babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.

Ya yi addu’a ga Allah Ya bai wa Jam’iyyar PDP nasara tun daga matakin ɗan majalisar jiha har zuwa Shugaban Ƙasa, domin ƙasar ta cigaba da shaida ɗumbin ayyuka cigaba.

“Ina kira ga ‘yan takarar da suka samu nasara da waɗanda suka faɗi a zaɓen fidda gwani, da su kasance masu haƙuri, tare da bada goyon bayan su domin nasarar jam’iyyar a 2023,” inji Sanata Kaita.

A nashi jawabin, ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar PDP Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su kasance masu zaven ɗan takarar da za su yi alfahari da shi idan ya lashe zaɓe a shekarar 2023.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya ce Jam’iyyar PDP a shirye take idan ta samu nasara ta tabbatar ta kori yunwa da APC ta kawo ta hanyar tsare-tsaren na wahalhalu data ƙaƙaba wa ‘yan ƙasar.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya hori al’umma da su duba cancanta su zaɓi nagartattun mutane, musamman wanda jam’iyyar ta kawo masu domin cigaba da kurvar romon dimokuraɗiyya.

Wakilin Jam’iyyar PDP na Ƙasa wanda kuma shine sakataren zaven sanatan ya ce, Ahmed Babba Kaita shine ɗan takara ɗaya tilo da ba shi da abokin hamayya da jam’iyyar ta saida wa tikitin tsayawa takara a ƙasar nan.

Ya ce sakamakon rashin abokin hamayya da kuma kaɗa ƙuri’ar amincewa da daliget suka yi, a don haka, jam’iyyar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *