Yadda ‘Super Tucano’ ya tilasta wa ISWAP naɗa sabbin kwamandodji

Daga BASHIR ISAH

A halin da ake ci ƙungiyar ISWAP ta yi wa shugabancinta kwaskwarima inda ta naɗa wasu ‘ya’yanta a muƙamai daban-daban don ci gaba da jan ragamar ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon hasarar kwamandojin da ta tafka biyo bayan hare-haren da jirgin yaƙi na Super Tucano ya kai wa mayaƙan ISWAP kwnan nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar kwamandoji da mayaƙan ƙungiyar da dama.

Jaridar PRNigeria ta kalato cewa, taron kwanaki biyu da ‘yan ISWAP suka gudanar ƙarƙashin jagorancin Sani Shuwaram, ya samu halarcin ‘yan Majalisar Shura da kwamandojin ‘yan ta’adda daga yankin Marte da Garal da Kayowa da Tumbum Murhu da Kurnawa da Chikun Gudu da Tumbumma da Kwalaram da Kirta da Wulgo, Jubularam da dai sauransu.

Sabbin kwamaandojin da ISWAP ta naɗa ɗin sun haɗa da Abubakar Ɗan-Buduma a matsayin mai kula da yankin Bakkassi Buningil da Doron Buhari; sai Muhammed Ba’ana a matsayin mai kula da yankin Kirta; Mohamet Aliamir a matsayin mai kula da yankin Kwalaram; Bakura Gana a matsayin mai kula da yankin Jubularam; Malam Musa a matsayin mai kula da yankin Jubularam; sai kuma Mohamadu Mustapha a matsayin mai kula da yankin Marte.

Bayanai sun tabbatar cewa taron nasu ya maida hankali ne kan rashin kwamandoji da mayaƙan da suka yi a sakmakon luguden wutar da jirgin yaƙin Super Tucano wanda sojojin Nijeriya suka tura ya yi wa mayaƙan ISWAP a sansanoninsu daban-daban a jihar Borno da wasu sassa a yankin Tabkin Chadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *