Yadda taron kacici-kacici da raba kyautuka akan harshen Hausa ya gudana a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Ɗaliban Hausa ta Nijeriya ta gudanar da taron gasar kaci-kaci da a tsakanin makarantun gaba da sakandire na jihar Kano, da kuma raba kyautuka ga zakarun gasar waƙoƙin Hausa da ya gudana a ɗakin taro na Convocation Arena da ke Jami’ar Bayero, Kano.

Taron dai ya mayar da hankali ne wajen wayar da kan matasa a kan illolin shaye-shaye a tsakanin matasa, waɗanda suka shiga gasar waƙar Hausar dai aƙalla sun kai guda 73. Taken taron shi ne, “Aiki da hankali’, wanda Mataimakin Gwamnan na Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ɗauki nauyin gudanarwa.

Wannan dai shi ne karo na biyu da wannan ƙungiyar ke shirya irin wannan gasa.

Babban mai jawabi Farfesa Abdullah Uba Adamu ya ce sauraron mawaƙan zamani musamman na Amerika yana daga cikin abubuwan da suke daɗa ingiza mutane su sha ƙwaya, saboda a cikin waƙoƙinsu su na maganganu a kan yadda ita ƙwayar ta ba su jarumtaka da ƙarfi kuma takamaimai waɗanda suke yin waɗannan su ake kira da Hipopas ko Rafas, wanda su ne suke fito da sunayen nau’o’in ƙwaya, akwai mawaƙa irin su Jeizy da Dokta drink DIG da sauransu.

“To waɗannan su ne suke nuna muhimmancin shan ƙwaya a cikin waƙoƙin su, kuma za ka ga suna shan ƙwayar, kuma masu kuɗi ne, za ka ga suna yin wata hayaniyar shiga, amma su mutanen mu sun manta cewa su fa a ‘yan lokon Mandawari ne ko lokon Soron Ɗinki.”

Don haka ya yi kira ga iyaye da lallai su kula kuma su sanya idanu wajen ganin an yaƙi wannan cuta ta shan ƙwaya musamman a tsakanin matasanmu.

Shi ma a jawabinsa, shugabn ƙungiyar Ɗaliban Hausa ta Nijeriya Ridwan Salisu Imam ya bayyana cewa duba da yadda al’umma ta tsinci kanta a cikin hali na shaye-shaye ta yadda za ka ga ‘ya’ya da ƙanne da yayye sun zama abinda suka zama, kai ya wuce yayye ya kai har matan aure, to ka ga abu ne da yake damun al’umma, “a matsayin mace na uwa a ce ta na shaye-shaye ka ga abin ya ɓaci.”

Kazalika abu na biyu shi ne sada zumunci da a tsakanin manyan makarantu na jihar Kano, sai kuma bunƙasa harshen Hausa da nuna muhimmancin harshen da riƙo da al’adun Hausawa shi ne dalilin shirya wannan taro.

Waɗanda suka lashe gasar kacici-kacicin su ne: Makarantar CAS ce ta lashe na ɗaya, inda ta samu kyautar kuɗi Naira 250,000.

Makarantar Aminu Kano wato LEGAL, ita ta lashe na biyu, inda ta samu kyautar kuɗi Naira 150,000.

Mataimakin Gwamnan Kano, Dr. Yusuf Gawuna (dama), tare da Farfesa Abdallah Uba Adamu a wajen taron

Sai Makarantar Sa’adatu Rimi ta lashe na uku, inda ta samu kyautar kuɗi Naira 100,000.

Waɗanda suka lashe gasar waƙa kuwa su ne: Ishaq Hamza Unguwar Mu’azu Kaduna ne ya lashe na ɗaya ya kuma samu kyautar kuɗi Naira 250,000.

Musa Muhammad Alle Argungu ya zama na biyu, inda ya samu kyautar kuɗi Naira 150,000.

Sai kuma Abba Muhammad Sagir Ɗan Hausa da ya kasance na uku, inda ya samu kyautar kuɗi Naira 100,000.

An kuma gabatar da lambar karramawa ga wasu zaƙaƙuran mutane dangane da gudunmawar da suke bai wa harshen Hausa.

Taron ya samu halartar Wazirin Kano wanda Ɗahiru S. Gidado ya wakilta, Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Isa Likita Muhd, sai Farfesa Aliyu Mu’azu Zariya da Farfesa Isa Mukhtar, sai alƙalan gasar kuwa su ne Malam Ado Ahmad Gidandabino MON da Kabir Abubakar sheshe da Musa BestSeller da sauran manyan masu ruwa da tsaki akan nazarin harshen Hausa.