Yadda Tinubu ya yaudari Obi ya yi takarar shugaban ƙasa don raba ƙuri’un PDP – Omokri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya bayyana cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yaudari ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi takara don a rage ƙuri’un ‘yan adawa.

Omokri ya ce Obi ba shi da wata hanyar samun nasara, domin ba shi da goyon bayan ‘yan ƙasa, amma zai iya raba ƙuri’un Jam’iyyar PDP.

A cewarsa, Tinubu ya yi amfani da amintattun ‘yan kasuwansa wajen yaudarar Obi ya shiga takarar shugaban ƙasa.

Omokri ya ƙara da cewa, Tinubu ya nuna gwaninta wajen fahimtar tunanin ‘yan uwa, waɗanda ya ce ba su da tawali’u don ganin ana juya su.

“Peter Obi ba shi da hanyar yin nasara. Ya rasa goyon bayan ‘yan ƙasa. Tinubu ya san haka. Amma ya yi amfani da amintaccen abokin kasuwancinsa, wanda ke son yin rawa a bainar jama’a da shi, ya yaudari Obi ya yi takara, ya san cewa ita ce kaɗai hanyar da za a rage yawan ƙuri’un PDP.

“Kuma mafi muhimmanci, Tinubu ya nuna gwaninta wajen fahimtar tunanin matsakaitan magoya bayan Obi. Ya san ba su da tawali’u don ganin ana wasa da su!

“Kuma har yanzu bai ƙare ba. A wurare irinsu Kaduna, APC na amfani da wannan dabara. Ba za su iya yin nasara da kansu ba. Don haka, suna ba da kuɗin yaƙin neman zaɓen gwamnan jam’iyyar Labour ne, da sanin cewa mutanen Kudancin Kaduna za su zaɓi Labour a cikin zuciya da kuma raba ƙuri’un PDP,” inji Omokri a shafinsa na sada zumunta.