Yadda wani matashi ya auri ’yan mata 9 a rana ɗaya

Wani matashi ɗan ƙasar Brazil, Arthur O Urso, ya shiga kundin tarihi na duniya bisa auren mata 9 a rana ɗaya saboda soyayya.

Rahotanni sun bayyana cewa, angon kyakkyawa ne sosai abin kwatance, wanda hakan ya sa kusan duka ’yan matan garin suka raja’a masa.

Arthur ya bayyana cewa, babban dalilinsa na yin haka shi ne don nuna tsantsar soyayya da kuma nuna adawa da auren mace ɗaya tilo.

Ya ƙara da cewa, ya yi haka ne don nuna soyayya da nuna adawa da auren mace ɗaya. An ɗaura auren ne a wani cocin Katolika da ke birnin Sao Paulo a ƙasar Brazil.

Tun farko dai Arthur ya auri wata mata mai suna Luana Kazaki, kuma a lokacin da suka tafi yawon cin-amarci ne suka yanke shawara kan Arthur ya ƙara auro waɗansu mata tara lokaci guda domin nuna cewa soyayya ta kowa da kowa ce.

Majiyoyi daga shafukan Intanet sun ce, Arthur da matarsa Luana an san su a fannin soyayya. Ma’auratan kuma sun shahara ta hanyar raba hotunan batsa lokacin da suke hutun cinamarcinsu a wani gari mai suna Cap D’Agde da ke Faransa wanda ya kasance bariki.

A cikin birnin na Faransa wanda ake ta magana a kansa. an haramta sanya tufafi, hakan ya sa dukkansu suka ji daɗin tafiya tsirara a wurare daban-daban na yawon buɗe-ido a birnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *