Yadda wasu likitoci suka sa wa mutum ƙodar alade

A karon farko wani ƙwararre a fannin tiyata a Amurka mai suna, Dakta Robert Montgomery ya ce, sun samu nasarar dasa wa wani mutum ƙodar alade, inda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen ƙarancin taimakon ƙoda da ake samu a wannan lokaci.

Ƙwaƙwalwar mutumin da aka sanya wa kodar tuni ta daina aiki, inda yake ci gaba da rayuwa da taimakon na’ura, lamarin da ya sa mutum ne da ƙwaƙwalwarsa ta daina aiki, lamarin da ya sa aka cire tsammani da shi.

Ita dai ƙodar da aka yi amfani da ita, ta wani alade ne da aka jirkita domin ta dace da halittar jikin ɗan Adam ta yadda ba za ta zama wani baƙon abu ba, balle ƙwayoyin kariya su yaƙe ta.

An gudanar da tiyatar a Jami’ar New York tsawon awa biyu, inda masu tiyatar suka haɗa da ƙodar aladen da ake bayar da jijiyoyin jinin ƙwaƙwalwar mutum domin tabbatar da ko za ta yi aiki yadda ake buƙata ko kuma akasin hakan.

Har yanzu ba a yi wa aikin kallo na tsanaki ba ko kuma a wallafa shi a mujallu da jaridu, amma akwai shirin yin hakan nan gaba.

Masana harkar lafiya sun ce, zuwa yanzu wannan ne aiki mafi girma da aka yi a wannan fanni. An tava yin gwajin irin wannan a kan birai, amma gwajin ba a taɓa yi ba a kan mutane.

Ba wani baqon abu ba ne amfani da sassan jikin alade domin dasa wa ɗan Adam. Tuntuni an jima ana dasa wa ɗan Adam bututun da ke kai wa zuciya numfashi.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai kuma wasu sassan da za su dace da ɗan Adam musamman a ɓangaren girma. Bayan gudanar da tiyatar, likitocin sun yi sama da kwana biyu suna nazarin yadda ƙodar ke aiki, sannan suna ci gaba da gwaje-gwaje iri-iri.

Ƙwararren likitan da ya jagoranci aikin, Dakta Robert ya shaida wa BBC cewa, “Mun riƙa bibiyar yadda ƙodar ke aiki na awanni, kuma tana aiki kamar ta ɗan Adam, wato duk abin da ƙodar mutum ke yi ita ma tana yi. Tana aiki sosai, kuma babu alamun za ta kawo wata matsala a nan gaba.

Zamanin a kashe wani a raya wani ya daɗe da wucewa kuma ba zai taɓa dawowa ba.” Ya ƙara da cewa, “zan iya cewa, kimanin kaso 40 cikin 100 na marasa lafiyar da suke asibiti za su rayu ta hanyar ƙodar alade. Muna amfani da alade a matsayin abinci, yanzu kuma za mu riƙa amfani da shi a matsayin magani – alade yana da ma’ana a rayuwarmu.”

Iyalan mutumin da aka dasawa ƙodar sun bayyana cewa, sun amincewa wa masu tiyatar da su gudanar da wannan aiki.

Wata likita da ke aiki a ɓangaren ƙoda da kuma ɓangaren kulawar gaggawa ta Hukumar Lafiya ta Birtaniya (NHS), Dakta Maryam Khosrabi ta ce, sun daɗe suna nazartar yadda za a riƙa yin amfani da wasu sassan dabbobi a jikin ɗan Adam, amma jin daɗinta a yanzu shi ne yadda waɗannan likitocin suka nuna cewa, abu ne mai yiwuwa.

Kakakin sashin kula da jini da na dashe-dashe na hukumar NHS ya ce, yadda sassan dabbobi za su riƙa yi wa ɗan Adam daidai yanzu muka sa a gaba, ya ce, “ci gaba da wannan aikin dashen yau da kullum ya tabbata.”