Yadda wasu matasan Kano 17 suka rasu a haɗarin mota, Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu matasa su 17 daga jihar Kano sun rasu sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su a babbar hanyar Zariya zuwa Kano yayin da suke komawa Kano daga Kaduna bayan halartar ɗaurin auren abokinsu.

Wannan mummunan al’amari ya auku ne da yammacin Asabar da ta gabata.

Bayanai sun tabbatar cewa wasu daga cikin matasan a nan take suka cika, yayin da wasunsu sai da aka dangana da asibiti kafin rai ya yi halinsa.

Majiyar Manhaja ta ce takwas daga cikin marigayan sun fito ne daga yankin Sani Mainagge a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar.

Sannan an yi jana’izar bakwai daga ciki a Lahadin da ta gabata a maƙabartar ‘Yan Hayis da ke Sani Mainagge Quarters.

Tuni dai Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan tare da bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar,Ganduje ya ce a madadin gwamnati da al’ummar Kano, yana jajanta wa jama’ar yankin Sani Mainagge a ƙaramar hukumar Gwale, ‘yan’uwa da abokan arziki bisa wannan babban rashi.

Tare da cewa yanzu babu abin da ya rage illa iyaka ci gaba da yi wa magabata addu’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *