Yadda Xi ke ziyarar aiki a ƙauyen Maona

Daga CMG HAUSA

Jiya Litinin da yamma, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki ƙauyen Maona, dake birnin Wuzhishan a lardin Hainan na ƙasar Sin, domin kara fahimta kan yadda ake inganta sakamakon da aka samu a fannin kawar da talauci a ƙauyen, da kuma ci gaba da aikin farfado da ƙauyen.

Cikin shekarun ke nan, an dukufa wajen kyautata muhallin ƙauyen Maona, domin raya harkokin yawon shakatawa, ta yadda zai kasance abun koyi a fannin neman farfaɗowar ƙauyuka a ƙasar Sin.

Mai fasarawa: Maryam Yang