Yadda ‘yan ƙungiyar asiri suka kashe ango a ranar aurensa a Delta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Al’ummar Kwale da ke ƙaramar hukumar Ndokwa ta Yamma ta jihar Delta sun shiga yanayi na jimami bayan tashin hankalin da ya danganci rikicin ƙungiyoyin asiri ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, yayin da wani mutum ya jikkata matuƙa.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, inda aka ce an harbe wani mutum a kusa da wani banki, yayin da aka tsinci gawar wani a mahaɗar Utagba-Uno.

Mutum na uku, wanda ya samu mummunan rauni, an garzaya da shi asibiti don samun kulawa.

Daya daga cikin waɗanda suka rasu shi ne wani ango wanda aka shirya aurensa a wannan rana.

“Yana tafiya tare da abokansa don siyan kayayyakin buƙatar biki ne lokacin da wasu da ake zargin ’yan ƙungiyar asiri ne suka kai masa hari,” in ji wani wanda ya shaida lamarin, amma ya nemi a sakaya sunansa.

Amaryarsa, iyalansa da abokansa sun shiga halin baƙin ciki mai tsanani yayin da ranar farin ciki ta koma ta tashin hankali.

Ba a samu damar jin ta bakin ’yan sanda ba, amma jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen sintiri tare da kafa shingaye a yankin domin hana ci gaba da tashin hankali.