Yadda ‘yan bindiga suka halaka fitaccen ɗan kasuwa a Bauchi

Daga WAKILINMU

A Talatar da ta gabata wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka halaka wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Tasi’u Abdulkarim a garin Tilden-Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Ƙanin marigayin, Isah Tilde, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun far wa yayan nasa ne a shagonsa na sayar da magunguna (Pharmacy) da ke kasuwar Tilden-Fulani wajajen ƙarfe 10 na dare, inda suka raba shi da kuɗaɗe masu yawa da wayoyoyinsa kana suka yi gaba da shi.

Ya ci gaba da cewa, daga bisani ɓarayin suka harbe marigayin a wani wurin da ba shi da nisa da shagon da suka ɗauke shi.

Kazalika, bayanan jama’ar yankin sun nuna an ji ƙarar bindiga a lokacin da ɓarayin suka shigo yankin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa marigayin ya rasa ransa ne a lokacin da ya yi ƙoƙarin tserewa daga hannun ‘yan bindigar.

Jami’in ya ce biyo bayan samun labarin shigowar ‘yan bindigar sai suka tashi rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro suka garzaya zuwa inda lamarin ya faru sannan suka ɗauki Alhaji Tasi’u zuwa babbar asibitin Toro inda a nan aka tabbatar da ya mutu.

Wakili ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ya ba da umarnin duka ofisoshin ‘yan sandan jihar maida hankali kan tsaronsu, tare da cewa su matsa bincike domin gano waɗanda suka kashe Alhaji Tasi’u don su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *