Yadda ’yan bindiga suka kama ɓarawo, suka miƙa shi ga hukuma

Wani al’amari mai cike abin mamaki ya faru, inda wasu ’yan bindiga a Jihar Katsina suka kama wani ɗan jari-bola yana sace-sace a ƙauyen da mutanen garin suka gudu suka bari.

Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin, wanda matashi ne da ya ƙware wajen cire rodika da ƙarafa daga ginin mutane a wani ƙauye.

Rahotannin sun rawaito cewa, ’yan bindigar sun kama matashin ne lokacin da suka fito sintiri a kan baburansu.

A wani bidiyo da aka samu, an ga ’yan bindigar suna gabatar da shi tare da ƙarafan da ya sata a gaban wani shugaban al’umma na ƙauyen.

Sai dai ba a iya tantance lokacin da aka naɗi bidiyon ba.

“Ba ka san sata laifi ba ce? Ka yi sa’a za mu miƙa ka ga hukuma, da kashe ka za mu yi,” inji ’yan bindigar.

’Yan ta’addan dai, waɗanda aka gani a bidiyon riƙe da muggan makamai, sun gargaɗi shugaban da ya tabbatar an hukunta ɓarawon daidai da doka don ya zama ala ga masu hali irin nasa.

Hakazalika, majiyar ta ce, ba wai kawai damƙa matashin suka yi ga hukuma ba, sun kuma tabbatar da cewa daga bisani jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi don a hukunta shi.