Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Masu haya da makwabtan mai gidan Obong Ete da ke Kalaba ta Kudu a Jihar Kuros Riba, sun ɗauki doka a hannunsu a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi masa mugun duka bisa zargin sata.
An tuhumi mai gidan mai shekaru 30 da haihuwa da laifin aikata ta’addanci ga masu hayansa tare da sace musu kayansu da suka haɗa da kayan abinci da kayan gida masu daraja.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, halin Obong Ete ya zama batu mai ɗaure kai, inda aka yi ta ƙoƙarin ya sauya halin amma ya ƙi.
“Ya daɗe yana yin hakan, kuma abin farin ciki ne ganin yadda a ƙarshe ya fuskanci wulaƙanci daga jama’a.
“Sau da yawa, shugabannin matasa da ƙungiyoyin ‘yan sintiri su na gano abubuwan da ya sata a gidansa,” in ji mazaunin John Akpan.
A yayin da ‘yan haya da makwabta ke shirin gudanar da ibadar ranar Lahadi, sun yi karo da Obong Ete, inda suka yi masa mugun duka da bulalar dawakai.
Bayan hakan, shugabannin matasan sun tilasta masa yin rantsuwa tare da yin alƙawarin daina sata da cin zarafi ’yan haya.
Obong Ete da aka yi masa duka da rauni, ya nemi afuwar abin da ya aikata kuma ya sha alwashin canza salonsa. Ya yarda cewa idan ya sake yin sata, maƙwabtansa suna da damar hukunta duk wani hukunci da suka ga ya dace.
Shugabannin matasan sun kuma zargi wani matashin da ke zaune tare da Obong Ete da laifin yin haɗaka tare da kore shi daga gidan mai gidan, inda suka gargaɗe shi da kada ya koma cikin al’umma.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sanda Irene Ugbo ta yi Allah-wadai da cin zarafi da aka yi wa Obong Ete, inda ta buƙaci da a riƙa kai rahoton irin waɗannan abubuwa ga ’yan sanda.