Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukuncin da matatar man Ɗangote ta yanke na rage farashin man fetur a daren ranar Asabar ya zo da ƙalubale ga ‘yan kasuwar man fetur da dama.
’Yan kasuwan da suka zanta da manama labarai, sun ce lallai rage farashin da matatar Dangote ta yi janye asara da ‘yan kasuwar mai da suka ɗaura ɗamarar shigo da man fetur daga ƙasashen waje ganin sun yi na matatun gida arha.
A ranar Asabar da daddare ne matatar man mai ƙarfin tace gangan 650,000 ta shaida wa ’yan Nijeriya cewa ta rage farashin manta daga N950 zuwa N890 kan kowace lita.
“A wani gagarumin yunƙuri na kawo sauƙin tattalin arziki ga ’yan Nijeriya, matatar man Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890 kowace lita, wanda zai fara aiki daga ranar Asabar.
“Wannan daidaita farashin yana mayar da martani ne ga ci gaba mai kyau a fannin makamashi na duniya da kuma raguwar farashin ɗanyen mai na ƙasa da ƙasa. Matakin da matatar ta Dangote ta ɗauka na nuna aniyar ta tafiya daidai da haƙiƙanin kasuwa da kuma tabbatar da cewa masu amfani da man sun amfana da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai na kasa da kasa,” inji wata sanarwa da Babban Jami’in Kula da Harkokin Kasuwanci na Matatar, Anthony Chiejina, ya fitar.
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, rage farashin man fetur zai yi matuƙar rage farashin man fetur a faɗin ƙasar, tare da samar da sakamako mai kyau a duk faɗin tattalin arzikin ƙasar.
Matatar man ta kuma yi kira ga ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar nan da su tabbatar an mika wa al’ummar Nijeriya fa’idar rage farashin man.
Duk da haka, ’yan kasuwa sun ce rage farashin yana da tasiri mai kyau da kuma mummunan tasiri akan kasuwancin su.
An tattaro cewa wasu ‘yan kasuwar da suka sayi kayan sa’o’i kaɗan kafin sanarwar za a tilasta musu su sayar da kasa da kuɗin da ake kashewa, tare da ciwo basussuka na miliyoyin naira.
A zantawarsa da manema labarai, mataimakin shugaban ƙungiyar masu sayar da man fetur ta Nijeriya, Hammed Fashola, ya ce rage farashin ci gaba ne mai kyau amma ko shakka babu zai shafi kasuwanci ta hanyoyi mara kyau da kuma kyau.