Yadda ’yan wasa da magoya bayansu suka fusata suka kashe alƙalin wasa

Wani alƙalin wasa ɗan ƙasar Salvadoriya ya gamu da ajalinsa sakamakon raunukan da ya samu a wani harin da ’yan wasa da magoya bayansu suka kai masa.

Jose Arnoldo Amaya ya kasance yana jagorantar wani wasa a makon da ya gabata, kuma ya nuna katin gargai na biyu ga wani ɗan wasa, inda ya kore shi saboda rashin ɗa’a.

Abin mamaki, wannan ya sa ‘yan wasa da magoya bayansu suka yi wa ɗan shekaru 63 ɗin mummunan duka, daga bisani kuma ya mutu sakamakon zubar jini na ciki.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Salvadoran dai ta yi gaggawar fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da wannan mummunar aika-aika da aka yi wa Amaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “a matsayinmu na tarayya mun yi watsi da duk wasu ayyukan rashin hankali da ake tadawa a wuraren wasanni daban-daban a ƙasar.”

Shi ma shugaban ƙasar Salvadoriya Hugo Carillo ya bayar da sanarwa a hukumance ta gidan talabijin na ƙasar don yin Allah wadai da wannan lamari mai ban tausayi.

Carillo ya ce, “a matsayin tarayya, mun yi watsi da abin da ya faru da alƙalin wasa Jose Arnoldo Amaya.”

“Kuma mun yi imanin cewa hukumomi za su iya gano waɗanda ke da alhakin kashe ran alƙalin wasan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *