Yadda zaɓe ke gudana a Mazaɓar Gwammaja

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

A Mazabar Gwammaja da ke Firamaren Masaƙa a Ƙaramar Hukumar Dala cikin birnin Kano.

Inda al’umma wannan yanki suka fito maza da mata suke kaɗa ƙuri’arsu,

Kayan zaɓe da malaman zaɓe sun isa tun ƙarfe 8 da ‘yan mintoci.

Da misalin ƙarfe 8:40 na safe ne dai aka fara kaɗa ƙuri’a.

Jama’ar wannan yankin suna ci gaba da shigowa cikin wannan mazaɓa domin gudanar da zabensu.

Haka dai labarin yake game da akwati na 27 da ke wannan makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *