Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

*Addinanci, ƙabilnci da ɓangaranci ba baqi ne a siyasar Nijeriya ba!
*Shin za a iya zuwa zagaye na biyu?

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A gobe Asabar ne za a gudanar da Babban Zaɓe a Nijeriya bayan shafe kusan shekaru huɗu na zango na biyu da shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya yi a kan kujerar mulkin ƙasar. Kowane zaɓe ya kan zo da yanayinsa kuma ya kan sha bamban da na bayansa.

Siyasar addinanci da ɓangaranci ko ƙabilanci ba baƙin abubuwa ba ne a Nijeriya. Don haka ba su daga cikin abubuwan da zaɓen 2023 ya bambanta da na baya.

Shin ta ina zaɓen 2023 ya sha bamban da waɗanda suka gabace shi? Editan Blueprint Manhaja, NASIR S. GWANGWAZO, ya yi nazari a taƙaice kan batun, kamar haka:

Yawan ’yan takara masu tasiri:

Tun daga Babban Zaɓen 1999 lokacin da Jamhuriya ta Huɗu ta fara, an fi sabawa da goyayya kan ’yan takara guda biyu kawai tsakanin Jam’iyyar PDP da wata babbar jam’iyyar da ke adawa da ita a kowane zaɓe, kamar APP, ANPP, CPC ko APC, domin hatta a Babban Zaven 2011, ANPP ba ta yi tasirin da za a saka ta a lissafi ba. To, amma a wannan karon na 2023 jam’iyyu guda huɗu ne ke da ’yan takarar da ake ganin za su iya yin tasiri.

Kodayake dai ba tasirin lashe ake nufi dukkan ’yan takarar za su yi ba, amma za su iya karkata zaɓen ta hanyar rage wa wata jam’iyyar yawan ƙuri’a, wanda hakan ka iya canja sakamakon zaɓen.

Jam’iyyun da ke yin takara mafiya ƙarfi su ne PDP, APC, NNPP da LP. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ke yi wa PDP takara, tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu ke yi wa APC takara, tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso ke yi wa NNPP takara, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Anambara Peter Obi ke yi wa LP takara a Babban Zaɓen na 2023.

An yi ittifaƙin cewa, uku daga cikinsu kowannensu yana da tasiri ko dai a jihar da ya fito ko kuma a yankin da ya fito. Za a iya cewa, Tinubu yana da matuƙar tasiri a yankin Kudu maso Yamma, inda ƙabilarsa Yarabawa suka fi yawa.

Haka nan Obi na da tasiri a yankin Kudu maso Gabas, inda ƙabilar Igbo ke da rinjaye. Shi kuwa Kwankwaso yana da tasiri a Jihar Kano, wacce ke da mafi yawan al’ummar a Tarayyar Nijeriya.

Za a iya cewa, ɗan takara ɗaya ne kawai babu ɓangaranci a takararsa, wato Atiku, amma takarar Tinubu da Obi za su iya shafarsa, saboda a baya Atiku da jam’iyyarsa ta PDP suna iya samun yawan ƙuri’u masu yawa a yankunan da suka fito.

Rashin haɗin kai a manyan jam’iyyu:

A baya ba a cika samun rarrabuwar a manyan jam’iyyu ba, rarrabuwar da za ta iya yin tasiri a Babban Zaɓen Nijeriya, to amma a wannan karon APC da PDP na fama da matsalolin cikin gida da za su iya taka rawa a sakamakon zaɓen.

Wannan ne a karon farko a Nijeriya da ake ganin Gwamnatin Tarayya ko Fadar Shugaban Ƙasa ba su tare da ɗan takarar jam’iyyarsu. Bugu da ƙari, a yayin da ake ganin gwamnati mai mulki ta yi baƙin jini a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari, maimakon babbar jam’iyyar adawa ta qasar, wato PDP, ta dunƙule waje guda, don samun damar kayar da jam’iyya mai mulki, wato APC, sai ita ma rikicin cikin gida ya dabaibaye ta, inda gwamnonin jam’iyyar biyar suka yi hannun riga da takarar tasu. Badaƙalar sabunta takardun Naira babbar abar misali ce.

A shekara ta 2015, manyan jam’iyyun adawa (ANPP, ACP, CPC da APGA) sun haɗe waje guda suka tunkari jam’iyya mai mulki a wancan lokaci (PDP), inda hakan ya ba su gagarumar nasarar kayar da ita a zaven. Amma a wannan karon babu dunƙulewar ’yan adawa a waje guda.

Ƙarfafa hasashen tafiya zaɓe zagaye na biyu:

A karon farko kenan tun bayan kafa wannan Jamhuriya ta Huɗu masu nazari ke ƙarfafa hasashen yiwuwar tafiya zagaye na biyu a Babban Zaven ƙasar. Wannan ya biyo bayan rashin tartibin tsayayyen ɗan takarar da ake ganin zai iya cika ƙa’idojin zaɓe na samun mafi rinjyane ƙuri’a kuma a lokaci guda ya samu kashi 25 na yawan ƙuri’un jihohi 24 daga cikin 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja ne.

Bayanai da nazari sun nuna cewa, har zuwa lokacin tafiya zaɓen, ɗan takarar APC, wato Tinubu, ba shi da cikakkiyar karɓuwa a mafi yawan jihohin Arewa 19, yayin da kuma a yankin jihohin Kudu maso Gabas nan ma ba shi da karɓuwa, sannan kuma dandazon al’ummar ƙabilar Igbo dake yankin Kudu maso Yamma, musamman a Jihar Legas, ba shi da goyon bayansu, saboda takarar da Obi ke yi.

Haka nan kuma ƙuri’un da Jam’iyyarsa ta APC ke samu a Jihar Kano, babu alamun za su samu a wannan karon, saboda da ma Shugaba Buhari ke samun ta a baya.

Shi ma Atiku ya samu tazgaro a karɓuwar takararsa, domin maimakon ya kwashe ƙuri’un da APC ta rasa, takarar Tinubu, Kwankwaso da Obi sun kawo masa cikas a yankunansu.

Su kuwa Kwankwaso da Obi ba a maganarsu a nan, domin ba su iya baza hajarsu ta yadda za su iya karɓuwa a sauran sassan ƙasar da ba daga nan suka fito ba ko kuma a ce jam’iyyunsu ba su da ƙarfin da suka zauna da gindinsu a can ɗin.

Rashin cikakkiyar aminta da ’yan takara:

A karon farko kenan dukkan ’yan takarar kujerar Shugaban Ƙasa a Nijeriya talakawan ƙasar ba su gama yarda da su ba bisa la’akari jin ra’ayoyin jama’a.

Bayanai sun nuna cewa, ’yan Arewa ba su gamsu da rawar da Atiku ya taka a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba wajen cigaban yankin, duk da cewa, a duka ’yan takarar shine wanda ba a kallon sa a matsayin mai ɓangaranci, addinaci ko ƙabilanci.

Shi kuwa Tinubu, ba ya ga zargin ƙabilanci ko ɓangaranci da yankunan Arewa da Kudu maso Gabas ke yi masa, batun gaskiyar lafiyarsa ya mamaye zukatan masu kaɗa ƙuri’a!

Yanzu dai a ce, ba a san maci tuwo ba, sai miya ta ƙare!