Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin sake zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a gobe, 15 ga Afrilu, 2023, jam’iyyun adawa da ’yan takara, a ƙarshen mako, sun ƙara zage damtse don samun galaba a zaɓen da kuma rage ƙarfin jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Ƙasa.

Za a cike zaɓen gwamnoni biyu, na sanatoci biyar, na majalisar wakilai 31 da kuma kujeru 57 na jiha.

Jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na 18 ga watan Maris, inda ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni 15, da Majalisar Dattawa 57, da ’yan majalisar wakilai 162 da fiye da kujeru 440 na majalisun jihohi.

Jam’iyyar PDP na da kujerun gwamna tara yayin da jam’iyyar LP da NNPP ke da guda ɗaya.

Makin da sauran jam’iyyu a Majalisar Dattawa su ne PDP-33, LP-8, NNPP-2, Social Democratic Party (SDP)- 2; All Progressives Grand Alliance (APGA) -1 da Young Progressives Party (YPP) -1.

A majalisar wakilai, PDP-105, LP-34, NNPP-18, APGA-4, SDP-2, African Democratic Congress (ADC) -2 da YPP-1.

Kamar yadda yake, jam’iyya mai mulki ce ke da mafi rinjaye wajen samar da shugaban da mataimakin shugaban majalisar dattawa. Da zaɓaɓɓun ’yan majalisar wakilai 162, jam’iyyar APC ita ma ke da rinjaye a majalisar wakilai ta ƙasa amma za ta iya fuskantar runtsi wajeb samar da kakakin majalisar wakilai da mataimakin kakakin da take so ba tare da goyon bayan jam’iyyun adawa ba.

Yayin da APC har yanzu ba ta da muƙamai a shiyyar, akwai ’yan tsiraru da suka fito daga shiyyoyin siyasa guda shida, wanda hakan ya ƙara rura wutar raɗe-raɗin cewa jam’iyya mai mulki za ta sake yin katsalandan kamar na zaɓen 2015.

Mafi yawan kujerun wakilai 31 suna cikin mazacun jam’iyyun adawa.

Za a sake gudanar da zaɓen na ’yan majalisar wakilai na mazaɓu 31 a jihohi 15. Akwa Ibom (2), Anambra (1), Bayelsa (1), Edo (1), Imo (1), Kano (2), Kebbi (2), Kogi (1), Oyo (2), Rivers ( 2), Sokoto (11), Taraba (1), Zamfara (2), Jigawa (1) da jihar Ebonyi (1).

Za kuma a gudanar da zaɓen Sanata ne a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

A Sokoto, za a sake gudanar da zaɓen na dukkan kujerun sanatoci uku – Sokoto ta Arewa, Sokoto ta Gabas da kuma Sokoto ta Kudu – inda a baya aka ayyana rashin kammalawan zaɓen.

Za a gudanar da zaɓe ne a rumfunan zaɓe 389 a dukkan ƙananan hukumomin jihar 23. Gaba ɗaya, akwai masu kaɗa ƙuri’a 227,743 da za su shiga zaɓen.

A jihohin Kebbi da Zamfara, za a gudanar da zaɓen ne a gunduma ɗaya na sanata kowacce – Kebbi ta Arewa da Zamfara ta tsakiya. Yayin da za a gudanar da zaɓen a jam’iyyu 23 a zaɓen Sanatan Kebbi ta Arewa, masu kaɗa ƙuri’a na PU 83 ne za su kaɗa ƙuri’ar zaɓen Sanatan Zamfara ta tsakiya. Suna da 13,243 da 47,277 da suka cancanci kaɗa ƙuri’a.

Samun rinjaye mai yawa yayin gudanar da wannan zaɓe na cike giɓi a vaingaren jam’iyyun adawa zai ba su damar yin tasiri mai yawan gaske wajen samar da shugabannin majalisar.

Idan za a iya tunawa, a 2015 an samu haɗaka tsakanin jam’iyyun adawa da wasu ’yan jam’iyya mai mulki, inda hakan ya sanya aka zaɓi Alhaji Abubakar Bukola Saraki a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa na Jam’iyyar APC mai mulki, inda kuma Chimaroke Nnamani na Jam’iyyar PDP ya zama mataimakinsa, abinda ba a taɓa gani a tarihi ba.

Yanzu ma a na fargabar hakan na iya afkuwa, idan har zaɓen cike giɓi na gobe ya yi wa Jam’iyyar APC tutsu!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *