Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Gwagwarmayar yaƙi da cin zarafin mata ta kwanaki 16 da aka saba gudanarwa duk shekara ta zo ta wuce, amma ba za a iya daina magana kan cin zarafi, cin zali da tauye haƙƙin da ake yi wa ‘ya’ya mata ba. Har sai ranar da aka wayi gari aka ce yau mata suna rayuwa cikin ‘yanci da kwanciyar hankali tare da maza abokan rayuwarsu, babu fargaba ko tsoron wani abu, ba a nan Nijeriya kaƙai ba har ma da duniya bakiƙaya.
ƙungiyoyin mata daban-daban a ƙasar nan sun shiga cikin wannan gangami na kwanaki 16 da aka gudanar a tsakanin ranakun 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba na wannan shekara, ƙarƙashin jagorancin Hukumar Kare Haƙƙoƙin ƙan’adam ta ƙasa. ƙaya daga cikin waƙannan ƙungiyoyi da suka gudanar da tsare-tsare don wayar da kan hukumomi, mata da sauran jama’a ita ce ƙungiyar Eƙual Access International, wacce kamar yadda ta saba, ta kasance akan gaba a wannan gangami da aka gudanar.
Kamar yadda yake bisa al’ada ta wannan gangami da ake yi na shekara-shekara, an gudanar da tarukan wayar da kai, tattaki zuwa Majalisar Dokoki ta Jiha domin isar da koke ga gwamnati, da riƙe kwalaye masu ƙauke da rubutu na irin kiraye-kirayen da mata ke yi, da kuma ganawa da manema labarai, don yaɗa manufofin gwagwarmayar da mata ke yi.
Ambasada Yakubu Gam da Caroline Edward suna da ga cikin waƙanda ƙungiyoyin Eƙual Access International da Mercy Corps ɓangaren kula da haƙƙokin mata da zaman lafiya a cikin al’umma suka yi wa koyarwa. Sun kuma bayyana wasu matsaloli da suka shafi cin zarafin mata waƙanda suka haƙa da auren wurin musamman ga yaran matan da ba su kai shekaru sha takwas ba. Auren dole, da hana mata gadon iyayensu, al’adun gargajiya da na addini da ke da cutarwa ga mata. Da kuma nuna fifiko ga ‘ya’ya maza fiye da mata.
Sun ƙara da cewa, akwai rashin bai wa mata cikakkiyar dama a harkar siyasa da shugabanci, a ɓangaren gwamnati da na gargajiya. Akwai batun yi wa yara mata fyaƙe, muzgunawa, cutarwa da rashin kula musamman a zamantakewar aure.
ƙaya daga cikin waƙanda bala’in cin zarafi ya rutsa da ita wacce take zaune a Jos a Unguwar Rayfield ta yi min bayyana cewa, mijinta ya tafi ya bar ta da yara takwas kimanin shekaru goma kenan, kuma ‘yan uwansa sun hana ta sake wani auren don ta samu mai kula da ita. Ga shi ba ya aiko mata da abinci, balle sutura ko kuƙin makarantar yara.
Sannan akwai wata yarinya da wani mutum ƙan shekara 45 ya yi wa fyaƙe a Unguwar Gyel da ke a ɓukur a ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, duk da an yi nasarar kai shi ga hukumar ‘yan sanda, amma daga bisani an sako shi saboda wasu dattawa sun shiga maganar.
A watannin da suka wuce an yi wa wata tsohuwa duka wanda har ya zama ajalinta a Zawan bisa ga zarginta da maita. Sannan ga batun safarar yara mata da sunan zuwa aikatau, wanda Jihar Filato ke kan gaba a cikin jihohin Nijeriya masu irin wannan halayya. A wani lokaci ma irin waƙannan ’yan mata da ake fita da su wasu garuruwa har tilasta musu shiga karuwanci ake yi.
Waƙannan kaƙan ne daga cikin munanan abubuwan cin zarafi da tauye haƙƙoki da ake yi wa mata da yaran mata a Jihar Filato da sauran jihohin Nijeriya. Wani abin takaici da ake cin karo da shi a wannan gwagwarmaya da ƙungiyoyin mata da masu kare haƙƙokin ƙan adam suke yi shi ne rashin samun goyon baya da haƙin kai daga wajen iyayen waƙanda aka ci zarafinsu da kuma na ƙin fitowa ko ƙin yarda su yi magana saboda gudun tsangwama da ɓatawa yaran suna. Wasu kuma akan yi masu barazana da nuna masu iko wanda ke sa su dole su yi shiru su janye maganar fyaƙe ko cin zarafin da aka yi wa ’yarsu daga kotu.
Sai kuma wani babban ƙalubalen da ake fuskanta na rashin haƙin kai hukumomi domin bai wa doka dama ta yi aikin ta. Akwai rashin kuƙi domin ƙaukaka ƙara daga ɓangaren wanda aka cuta. Da halin ko-in-kula daga ɓangaren jami’an tsaro da masu shari’a, wanda daga ƙarshe ake sakin waƙanda aka kama da laifi, kuma su koma su cigaba da cutar da jama’a. Sannan ga matsalar rashin isasshen wayar da kai akan hanyoyin da ya kamata a bi domin samun adalci.
Daga cikin dalilan da sukan jawo cin zarafin mata akwai matsalar talauci da rashin ingantacciyar kulawa daga iyayen.
Akwai shaye-shayen ƙwayoyi, rashin zuwa makaranta, da miyagun abokai ko ƙawaye. Sai kuma rashin aikin yi ko sana’a.
Yanzu haka dai wannan gwagwarmaya da ƙungiyoyi masu zaman kansu tare da haƙin gwiwar jama’ar da suka yi wa bita za ta cigaba domin faƙakar da jama’a illolin cin zarafin mata da ƙananan yara, ta hanyar tattaunawa da wayar da kan malaman makarantu, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin mata da matasa.
Sannan an yake shawarar koyawa mata da matasa sana’o’in dogaro da kai irinsu ƙinki da yin soye-soyen kayan ƙwalama ga girke-girke a Gyel da ke ɓukur, inda wasun su ma har sun gama koyo sun karɓi shaidar gamawa.
Shugabar ƙungiyar Lauyoyi Mata ta FIDA, reshen Jihar Filato Barista Naankus Fyaktu ta bayyana cewa babban aikin ƙungiyar shi ne kare haƙƙokin mata da ƙananan yara daga kowane irin nau’i na cin zarafi, muzgunawa, cutarwa, lahani, cin mutunci da rashin kulawa a zamantakewar aure. Kamar yadda suka saba su kan shigar da ƙara kotu don tabbatar da adalci, da yin sulhu a harkokin zamantakewar iyali, wanda kuma ya shafi barazana ga rayuwa da ya haƙa da duka har ya kai ga kisa sai a haƙa su da hukumar ‘yan sanda domin gudanar bincike da shigar da ƙara a kotu.
A nata ɓangaren shugabar ƙungiyar mata ‘yan jarida reshen Jihar Filato Misis Nene Dung tag bayyana irin haƙin kan da suke samu da sauran ƙungiyoyin mata ‘yan gwagwarmaya kamar su FIDA da Hukumar Samar da Daidaito a Tsakanin Jinsi wato Gender and Eƙual Opportunities Commission, Eƙual Access International, da saura ƙungiyoyi masu zaman kansu. Yayin da suke cigaba da wayar da kan jama’a ta cikin shirye-shiryen da suke gabatarwa a rediyo da talabijin, da rahotanni bisa ga abubuwan da ke faruwa da kuma bin diddigi har sai an zartar da adalci.
Idan za a iya tunawa, Jihar Filato na daga cikin jihohi na farko-farko da suka amince da kafa dokar yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara, kodayake masu ruwa da tsaki a wannan gwagwarmaya na ganin gwamnati na jan ƙafa wajen aiki da dokokin, da rashin nuna ƙwarin gwiwa. Sai dai Mataimakiyar Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, Misis Kachollom Lucy Michael ta bayyana cewa gwamnatinsu a shirye ta ke domin ta ba dama a dama da mata yadda ya kamata. Kuma suna da shirin ba da tallafi da koyawa mata da matasa sana’o’i domin samun abin dogaro da kai.
Sannan yaran da suka daina zuwa makaranta saboda matsalar rashin kuƙi musamman a matakin firamare da makarantun gaba da firamare za a yi ƙoƙarin mayar da su makaranta. Ba ya ga ofishin kula da walwalar al’umma na ƙaramar hukumar, za kuma a ba da damar buƙe ofishin kula da ƙorafe-ƙorafe na ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Gwagwarmayar matan harwayau ta samu nasarar samun haƙin kai da goyon bayan shugabannin al’umma a matakin unguwanni da ƙauyuka, da shugabannin addini, da na matasa, waƙanda su ma suka shiga cikin tarukan da aka riƙa yi, da nuna goyon bayansu. Yanzu haka ma akwai aƙalla matasa maza 120 da suka ba da kansu wajen bincike da sa’ido wajen zaƙulo masu aikata fyaƙe a cikin unguwannin Jos, musamman a yankin Gyel, inda wannan matsala ta yi ƙamari, domin gurfanar da su gaban hukuma.