Yadda za a magance maiƙon fuska

Daga AISHA ASAS

Uwar gida za ta iya magance maiƙon fuska da kanta ba sai ta je ga likita don ya ba ta magani ba. Ta ya ya?

Wankin fuska:
uwar gida za ta ga wannan a matsayin wasan yara, a tunanin ta ba zai zama hanyar kawar da maiƙon fuska ba, sai dai abin da ba ta sani ba kamar yanda yawan wanke fuska ka iya ƙara maigon fata, haka zalika ƙarancin sa zai magance yawaitar maiƙo. Uwar gida ta wanke fuskarta sau biyu a rana da sabulu masu taushi, kamar gilasarin.

Amfani da zuma:
Zuma na ɗauke da sinadarin da ke jiƙa fata ba tare da ta sa ma ta maiƙo ba, shi wannan sinadari na janye maiƙo ba tare da ya bar wata alama. Ana amfani da zumar ne ta hanyar shafa ta zumar wadda ba ta da haɗi a fatar, a barta ta bushe tsayin mintuna goma, sai a wanke da ruwa mai ɗumi.

Haɗaɗɗiyar laka (cosmetics or healing clays) :
Wani haɗin laka ne da ake siyarwa a shagunan siyar da kayan gyaran fata na bature. Shi wannan haɗin ya na tsotse maiƙon fata, kuma ana amfani da shi wurin magance matsalolin fata masu yawa. Shi wannan haɗi kan zo a nau’i daban daban, amma mafi shahara wurin amfani shine, Wanda ake kira da ‘franch green clays’. Wanda yake zuwa a gari. Yanda za ki haɗa shi kuwa shine, ki ɗibi ƙaramin cokali ɗaya na garin, ki haɗa shi da ruwa mai tsafta. Ki juya shi, sannan ki ba shi dama ya zama ɗaya shi da ruwan. Amma fa uwar gida ta sani, ruwan daidai misali, wanda idan ya haɗe zaiyi kauri sosai. Ki shafa haɗin na ki a fuska, Sai ki bar shi har ya bushe, sannan a wanke da ruwa mai ɗumi, sannan ki sanya tawul mai kyau ki goge fuskar. Uwar gida yana da kyau ki san cewa, ba fa yanda kike goge sauran jikinki ne za ki goge fuska ba. Fuska za ki dinga buga tawul ɗin a hankali ba goga wa ba.

Ƙwai da lemun tsami:
Farin cikin Kwai da lemun tsami suna da sinadarai da ke rage girman ramukan gashi. Hakan kuwa hanyace ta rage yawaitar maiƙo. Yanda za ki haɗa wannan magani shine; ki fasa kwai ɗaya, ki cire ƙwaiduwar, za ki yi amfani da farin, sai ƙaramin cokali ɗaya na ruwan lemun tsami, ki shafa a fuska, ki ba shi dama ya bushe sosai kafin a wanke da ruwa mai ɗumi. Sai a goge da tawul.

Alobera:
Mun fi sanin alobera a magance matsalar ƙunar fata da sauran abin da ya shafi irin wannan a fata. Sai dai bincike na ƙwararu ya tabbatar da alobera na ɗauke da sinadarin da ke hana yawaitar maiƙon fata da kuma varewar fata. Za ki shafa ta ne da dare kafin barci, ki kwana da ita, sannan ki wanke da safe da ruwan ɗumi. Abin lura; idan ba ki tava amfani da alovera ba, zai yi kyau ki shafa kaɗan a fatar hannunki, tsayin awanni don tabbatar da fatar ki na karvar ta ko ba ta so.

Tumatir:
Tumatir na ɗauke da sinadari mai suna salisalik ased (salicylic acid), wannan sinadari da ke cikin tumatir zai taimaka wurin tsotse maiƙon da ke cikin fata, kuma ya cire daukar da ke toshe ramukan gashi. Yanda za ki haɗa shi; za ki samu tumatir mai kyau ɗaya, ki niqa shi, kafin ki sa ƙaramin cokali na sukari a ciki, sai ki dinga ɗiba kina gurza shi a fuska, za ki jima ki na goga shi, amma ba da ƙarfi ba. Idan uwar gida ta tabbatar ko ina ya samu, kuma ya gogu, to sai ta bar shi tsayin mintuna biyar kafin a wanke da ruwa masu ɗumi, sai a goge da ƙyale mai tsafta da laushi.

Daga ƙarshe ina so uwar gida ta san cewa, fata mai maiqo ba illa ba ce sosai kamar yanda muke ɗaukarta, asalima za ta yi ma ki amfani a lokacin tsufa. Saboda za ta hanaki saurin nuna tsufa kamar yanda mai busassar fata za ta yi.