Yadda za a magance matsalar kogon haƙora (1)

Daga AISHA ASAS

Matsalar kogon haƙora ko in ce ramin haƙora matsala ce da ta zama ruwan dare a tsakanin mutane, kasancewar akan same ta a wurin manya da yara kai har ma a tsofaffi.

Matsalar dai ta zama wata wutar daji da ke saurin tsananta ba tare da mai ita ya ankara ba, kasancewar saurin tsananta da ta ke yi. Sai dai abin da ba mu sani shine, matsalar na ta’azzara ne albarkacin wasu ababen da muke yi da ke taimaka wa cutar wurin yaɗuwa, kamar yawan barin baki a bushe, rashin sinadarin fluorine (sanadari ne da ke hana haƙora lalacewa.

Kuma anan samunshi har ta wasu daga cikin man baki da muke amfani da shi, sannan yakan samu har cikin nau’ukan tsiro akwai waɗanda ke iya wadata mu da wannan sinadarin).

Akwai kuma cin abincin da ke da kafiya, waɗanda ke samun maɓuya a haƙora, kamar nama, cin su a kwanta lokuta da dama kafin ka tashi sun zama ƙwayar cuta da ita kanta za ta gina rame a haƙoran.

Shi ya sa yake daga cikin mafita, jinkirta kwanciya bayan ka tabbatar da wani abinci ya samu maɓuya a haƙoranka, har sai ka bi ‘yan dabaru da ba za su cutar da dasashin haƙoran ba wurin ganin ka fitar da shi kafin ka wanke baki, ka kwanta.

Kazalika wannan matsala ta ɓuyar abinci na iya haifar da warin baki, kasancewar abincin na rubewa ne har ya haifar da ƙwayoyin cuta, wanda wannan ruɓewar kan iya bayyanar da kanta ta hanyar canza iskan baki.

Baya ga haka, kogon haƙora na samun wurin zama idan ka kasance ma’abuci ciye-ciye, kuma ba mai yawan wanke baki ba. Ko da kuwa ba masu yawan shiga cikin haƙoran ba ne.

Duk da cewa, yana da matuƙar muhimmanci a hanzarta ganin likita idan irin wannan matsala ta samu tun da wuri, shafin kwalliya na wannan sati zai kawo ma ku hanyoyin da za a iya bi cikin sauƙi don magance matsalar kogon haƙora ko yin rigakafi daga samun matsalar.

  1. Yanke alaƙa da kayan zaƙi:

Kayan da ke da yawaitar suga a ciki na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da matsalar ramen haƙora, kuma suna ɗaya daga cikin dalilan samuwar ta tun daga farko.

Don haka tsagaita kwankwaɗar zaƙi hanya ce mai matuƙar muhimmanci da za ta iya zama silar rabuwa da kogon haƙora, ko kuma ta hana samuwar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *