Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da saduwa a wani makon.

A makon da gabata mun fara kwararo jawabi a kan yadda namiji zai ɓullo wa maganar ƙaro aure. Mun fara kawo wasu shawarwari yadda za a kauce wa fitina. Yanzu za mu tashi daga inda muka fara a makon da ya gabata.

Abu na gaba, akwai wani ma tun yana neman auren matarsa ta fari zai ta yi mata zaƙin bakin ba shi ba yi mata kishiya. Kai da ba ka san me Allah ya shirya maka ba a rayuwa. Ba ka san me zai faru a gaba ba. Amma kake yanke irin wannan hukunci. Sai kuma idan Allah ya rubuta maka ƙara mata ko mata, sai ka fuskanci bore daga matarka. Saboda ita ta riga ta gama sakankancewa.

Wata har mutane ta gama yaɗa wa. Idan ba ka ci sa’a ba ma, wata har abada za ta yi ta kallonka a matsayin macuci, ma ci amana, ko mayaudari. To ɗanuwa, me gari ya waya? Garin gyaran gira kuma ai ba a rasa ido ba. Duk da maganarka cikin giyar so ka yi ta. Kuma a lokacin da ka yi mata wannan alqawarin har cikin ranka ka yi shi. Amma ba ka san ƙadddararka ko tata ba. Wa ya aike ka ka yi alƙawari a kan abinda yake gaibu? Ko a wajen Allah abinda ka yi ba dai-dai ba ne. A matsayinka na mumini kullum sai ka zam a cikin shirin jarrabawa daga Allah.

Don haka sai a kiyaye. Ko a raha ka dinga ɗan shigar mata da zancen fa ba ita kaɗai ba ce. Allah zai iya jarrabarka da ƙaro wata. Kuma ka sani, kaso ma fi yawa na mata da suka fi bore lokacin da za a musu kishiya su ne waɗanda al’amarin ya zo musu a ba-zata. Wato waɗanda ba su tava zaton za a ƙaro musu kishiya ba. Ko waɗanda mijin ya ɓoye musu sai a gari suka ji.

Waɗannan abubuwa da na zano a sama su ne kamar shimfixa ko harsashin da ya kamata ka dasa. To idan kuma ka samu matar da za ka ƙaro a matsayin ta biyu, kun tattauna har magana ta kai ga iyaye, batun auren ya zo. To Hausawa sun ce ranar wanka ba a voyon cibi.

Haka rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A nan wanne salo ya kamata ka bi don ganin ka isar wa matarka saƙon cikin lumana ba tare da an samu hargitsi ba? Kuma wanne salon taku za ka ɗauka don ganin ba ka tayar wa da uwargida kishinta ba kuma ba ka tauye wa amarya haƙƙoƙinta ba? Ga wasu shawarwari kamar haka:

Da farko dai ɗanuwa mai nufin ƙaro aure ka sani: Shi ƙaro aure ba cin amana ba ne ko cin fuska kamar yadda wasu matan suke ɗauka. Cin amanar shi ne ka auro wata ka wulaƙanta ta. Kada ka juya wa matarka baya a lokacin da ka nufi ƙaro aure.

A lokacin ta fi buƙatar ka fiye da kowanne lokaci. Idan ta ga ba ka canza mata ba za ta saki ranta da sha’anin ƙaro auren naka. Kuma ko bayan matar ta zo yi ƙoƙarin ganin ba ka canza mata ba.

Ka gaya mata kai tsaye: A lokacin da kake son karo aure ka zama kai ne za ka gaya wa matarka kai tsaye. Idan ba za ka iya ba, ka wakilta wani ko wata da ka amince wa ya faɗa mata. Kada ka bari ta ji a gari. Hakan zai iya harzuƙa ta.

Kada ka yaudare ta: Ka fito fili ka gaya mata gskiya kada ka yaudare ta. Ka faɗa mata za ka ƙara aure ne don raya sunnah da bin umarnin Allah (SWA) da ya ce a ƙaro idan da hali. Ba wai don gazawarta ba Kada ka yi mata daɗin bakin da wasu maza kan ce wa matarsu za su kawo mata mai taya ta aiki ko raino. Daga ƙarshe kuma abun ya zama matsala.
Ka lallashe ta. Kuma ka yi alƙawarin ba za ka juya mata baya ba.

Ko da Allah ya nufe ka da son wata fiye da wata, ka yi ƙoƙarin dannewa a gabansu saboda gudun ta da fitina. Sannann ka tabbatar ka zama mai adalci a kan duk wani abu da za ka saya ka ba su.

Ka nuna wa Amarya uwargida na da muhimmanci ta girmama ta. Haka uwargida ma ka nuna mata muhimmancin Amaryar.

Kar ka bi sahun maza mayaudara masu kushe uwargida a gurin amarya. Sannan su zo gida su ce da uwargida ai ba son Amaryar suke ba kaddara ce ta sa zai ƙaro aure.

Ka yi ƙoƙarin kyautata mata ta hanyar sabunta mata sutura, kayan kwalliya, har ma da kayan gida idan da hali.

Ka rage ɗoki da rawar kai a gabanta. Hakan zai motsa mata kishi kuma ya harzuƙa ta. Banda kira ko hirar wasaf har tsakar dare ko asuba.

Dole ka ƙara haƙuri kan haƙuri domin wannan sabon al’amari ne. Uwargida tana jin kanta, Amarya ta shigo da rawar kai.

Kada ka yarda ka tauye haƙƙin Amarya saboda kana ƙoƙarin lallashin Uwargida. Dole ka zama namiji ka nuna mata cewa ita ma wannan matarka ce tana da haƙƙoƙi a kanka. Rashin yin haka tun a farko zai iya jawo matsala nan gaba.

Ka tabbatar Amaryarka ta zama mai girmama uwargidanka. Haka kuma kada ka sake yaran uwargida su raina Amarya. Saboda kawai tana auren ubansu. Ka sani tarbiyyar ‘ya’yanka tana da matuƙar muhimmanci. Kada ka bari a kassara musu ita saboda kishi.