Yadda za ka ɓullo wa maganar ƙaro aure

Tare da AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum wa rahmatullah. Masu karatu sannunku da jimirin karatun shafinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Ina muku godiya fatan alkhairi kamar yadda koyaushe kuke yi min ta hanyar kiran waya ko saƙon tes. 

Rubutun wannan mako dai na maza ne. Za mu yi magana a kan matakan da ya kamata ‘yanuwa maza su ɗauka yayin da suke da nufin ƙaro aure. Ko kuma gwari-gwari a ce ƙaro mata daga ɗaya zuwa biyu, har ma sama da haka.

Maza da yawa suna kokawa a kan yadda matansu na gida ke birkice musu yayin da suka nufaci wannan ƙudiri na alkhairi na ƙaro mata. Wasu ma saboda tsoron tashin hankalin matar gidan da gudun abinda kan je ya zo bayan auren, sai namiji ya haƙura da ƙaro auren gabaɗaya.

Duk da tsananin buƙatarsa ta karo auren. Shi ya sa wannan makon na zo wa da ‘yanuwa masu nufin ƙarin aure wasu shawarwari da za su iya taimaka musu don samar da zaman lafiya da maslaha a lokacin da suka ƙudurci yin wannan jan aiki na ƙaro aure. 

Ɗan uwana, kafin na fara zubo ruwan shawarwari, ya kamata ka sani. Yadda ka gyara gadonka haka za ka ji daɗin kwanciya a kai. Ma’ana: Yadda ka tsara rayuwar gidanka yana da matuƙar tasiri a kan yadda za ka samu kwanciyar hankali ko akasinta. Don haka ka tabbbatar ka yi wa kanka shimfifa mai kyau.

Kamar yadda mu ka san ba za a yi gini a kan iska ba, dole sai an kafa harsashi, haka ma aure yake. Sai an sa harsashi sannan ake ɗora gini a kai, sannan ya yi ƙarko. To zaman aure tamkar misalin wannan ginin ne. Matarka ta fari ita ce misalin wannan harsashin ne. Idan ya yi ƙarko, sauran gini ma ya yi ƙarko. Idan bai yi ba kuma, komai ya lalace. 

Da farko dai ɗan uwa ka sani, gina aminci da yarda a tsakaninka da matarka ya fi komai sanya nutsuwa a zukatan ma’aurata. Kuma ya kasance ka gina hakan tun kafin ka ƙudurta nufin ƙaro aure. Ta yaya za ka gina aminci tsakaninka da iyalinka? Amsar mai sauƙi ce. Ka zama zaƙaƙurin namiji mai kula da dukkan haƙƙoƙinta har ma da kyautata mata a kan abinda ba ma haƙƙinta ba ne.

Ka zama mai ba ta kariya a kan dukkan wani abu ko mutum da zai keta mata alfarma ko da kuwa ‘yanuwanka ne. Amma ba a ce ka fifita ta a kan danginka ba. Hakazalika ka zama mai mata uzuri. Sannan kada ka dinga yi mata ɓoye-ɓoye a kan komai.

Ka daure ka dinga gaya ma ta gaskiyar lamari. Ko da ƙaryar za ta fi yi ma ta daɗi. Waɗannan halaye za su ƙara soyayyarka a zuciyarta. Kuma za su sanya hankalinta ya ƙara kwanciya da kai. Ta ji a ranta kai ɗin nan mutumin kirki ne. Kuma ba azzalumi ba ne. Ta sakankance da duk abinda za ka yi, ba za ka cutar da ita ba. Ko da zancen ƙarin aure ka ɗauko, ba za ta yi bore ba. Ya kamata maza su sani.

Bayan zafin kishi, babban abinda ke sa mata ƙin kishiya shi ne: tsoron kada a auro wata mijin ya juya mata baya. Amma idan ka samar da hakan tsakaninka da ita, za ta samu nutsuwar ba za ka cutar da ita ba. 

Na biyu, kamar yadda Hausasawa suka ce: “tun ran gini, tun ran zane”. To hakan yake. Ka tabbatar da kyau bai ruɗe ka ba wajen zaɓen abokiyar rayuwa. Ka zaɓo mace nutsattsiya mai ilimi da tarbiyya. Shi ne za ka more rayuwar aure. Kuma ba za ta rusa maka gidanka ba da sunan bore da kishi ba idan za ka ƙaro aure’.

Abu na uku shi ne: ka guji yi wa matarka musamman uwargidanka daɗin bakin daga ita ba wata. Wani ma tun yana neman auren matarsa ta fari zai ta yi mata zaƙin bakin ba shi ba yi mata kishiya. Kai da ba ka san me Allah ya shirya maka ba a rayuwa. Ba ka san me zai faru a gaba ba. Amma kake yanke irin wannan hukunci.

Sai kuma idan Allah ya rubuta maka ƙara mata ko mata, sai ka fuskanci bore daga matarka. Saboda ita ta riga ta gama sakankancewa. Wata har mutane ta gama yaɗa wa. Idan ba ka ci sa’a ba ma, wata har abada za ta yi ta kallonka a matsayin macuci, ma ci amana, ko mayaudari. To ɗan uwa, me gari ya waya? Garin gyaran gira kuma ai ba a rasa ido ba.

Duk da maganarka cikin giyar so ka yi ta. Kuma a lokacin da ka yi mata wannan alƙawarin har cikin ranka ka yi shi. Amma ba ka san ƙadddararka ko tata ba. Wa ya aike ka ka yi alkawari a kan abinda yake gaibu? Ko a wajen Allah abinda ka yi ba dai-dai ba ne. A matsayinka na mumini kullum sai ka zam a cikin shirin jarrabawa daga Allah. Don haka sai a kiyaye. Ko a raha ka dinga ɗan shigar mata da zancen fa ba ita kaɗai ba ce.

Allah zai iya jarrabarka da ƙaro wata. Kuma ka sani, kaso ma fi yawa na mata da suka fi bore lokacin da za a musu kishiya su ne waɗanda al’amarin ya zo musu a ba-zata. Wato waɗanda ba su tava zaton za a ƙaro musu kishiya ba. Ko waɗanda mijin ya ɓoye musu sai a gari suka ji. 

Waɗannan abubuwa da na zano a sama su ne kamar shimfiɗa ko harsashin da ya kamata ka dasa. To idan kuma ka samu matar da za ka ƙaro a matsayin ta biyu, kun tattauna har magana ta kai ga iyaye, batun auren ya zo. To Hausawa sun ce ranar wanka ba a ɓoyon cibi.

Haka rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A nan wanne salo ya kamata ka bi don ganin ka isar wa matarka saƙon cikin lumana ba tare da an samu hargitsi ba? Kuma wanne salon taku za ka ɗauka don ganin ba ka tayar wa da uwargida kishinta ba kuma ba ka tauye wa amarya haƙƙoƙinta ba?

Ga wasu shawarwari da zan ba wa maza a kan yadda za su ɓullo wa maganar ƙaro aure. Amma sai mako na gaba da yardar Allah za mu kawo ci gaban wannan bayani. Sai an jima.