Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce majalisar dokokin ƙasar za ta gudanar da muhawara a fili kan ƙudirin gyara harajin shugaban ƙasa Bola Tinubu a gabanta domin jin ra’ayin ’yan Nijeriya.
Adaramodu, ya ce galibin waɗanda ke sukar ƙudirin a kafafen yaɗa labarai ba su san haƙiƙanin amfanin harajin ba, kuma suna tunani ne bisa aƙidar cewa duk wani haraji zai ɗora wa mutane nauyi, ya ce, “Ban ga wani abu da zai kawo koma baya a cikin ƙudirin gyara harajin ba.”
Sanata mai wakiltar mazaɓar Ekiti ta Kudu ya zanta da manema labarai a mahaifarsa ta Ilawe Ekiti a yammacin ranar Asabar bayan bikin ranar haɗin kan Ilawe tare da ƙaddamar da asusun tallafi har na miliyan N500 domin fara gudanar da aikin inganta asibitin koyarwa a tsakanin al’umma.
Sukar sun biyo bayan ƙudurorin gyara harajin da fadar shugaban ƙasa ta tura wa majalisar dokokin ƙasar.
Amma Adaramodu ya ce, “Shin waɗanda ke sukar dokar sake fasalin haraji sun gansu? Dokar sake fasalin haraji da za ta ware masu ƙaramin ƙarfi daga biya, shin za ku ce wancan ya koma baya? ƙudirin sake fasalin haraji wanda zai tabbatar da cewa babu haraji biyu ko yawa, ban ga wani abu da ke da koma baya ba game da lissafin sake fasalin haraji.”