Yadda za mu inganta sana’armu don yaƙi da talauci

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kamar da wasa aka fara sanya hotunan kayan sayarwa da sana’o’i a zaurukan sada zumunta, ana aikawa da wanda aka saya, bayan an biya kuɗin ta banki, a motocin haya ko ta hannun wasu amintattu, yanzu wannan hanyar tallata kasuwanci ta zama babbar harka da miliyoyin ’yan kasuwa maza da mata ke samun kuɗaɗe masu yawa da abin rufin asiri.

Da dama daga cikin waɗanda suke wannan kasuwanci ko dillanci, basu da rumfa ko shago, a gida suke ajiye kayansu, sai an saya sannan su fitar da shi zuwa tasha. Wasu kuwa ma ba su da kayan a gida, dillanci kawai suke yi, idan sun samu mai saya sai su aikawa masu kayan kuɗin su da lambar wayar wanda ya saya don a aika masa, yayin da su kuma suke cire ɗan abin da suke qarawa a kai na riba, a matsayin nasu kason. Wannan shi ne sabon salon kasuwanci na zamani, da ake kira da turanci Online Business.

Kasuwanci mafi sauqi, da ba ya buqatar jari mai yawa, ko ma ba sai da jarin ba, matuƙar za ka samu waɗanda za su amince maka su riqa baka sarin kaya a sauƙaƙe, kai kuma kana qara naka a kai, kana neman masu saye. Ba ka buƙatar kuɗin kama hayar shago a cikin kasuwa ko a wata fitacciyar Filaza, kuma kasuwanci mai sauƙin asara, saboda a mafi yawan lokuta sai an biya kuɗin kaya sannan a aika. Sakamakon yadda wasu marasa amana ke nuna rashin gaskiya, wajen riqewa masu kaya kuɗi ko rashin biyan bashi a kan lokaci.

Bincike ya nuna cewa ’yan Nijeriya ne kan gaba a duk faɗin Afirka wajen yin wannan harkar kasuwanci ta yanar gizo ko ta zaurukan sada zumunta, saboda ƙwazon da suke nunawa da kishin kansu, don su canja labarin rayuwarsu, a maimakon su zama masu roqo da jiran a basu, ko zauna gari banza. Nijeriya na da ɗimbin matasa da yawansu ya kai kimanin kashi 53.40 cikin ɗari na ’yan Nijeriya miliyan 193, waxanda ba su da takamaimiyar sana’a ko wani aiki da ake biyansu albashi. Masu nazarin harkokin kasuwanci na ganin wannan na da nasaba wajen ƙaruwar mata da matasa a cikin wannan kasuwanci da dillancin kaya ta hanyar wayar salula.

Duk da nasarori da a baya na ambata da wanda jama’a da dama suka tabbatar kasuwancin onlayin yana kawowa, akwai ƙalubale da dama da ake cin karo da su, kamar yadda yake a kowacce harka ta rayuwa. Wasu matsaloli ne ake cin karo da su sakamakon yadda wani ya gagara yin abin da ya dace a lokacin da ake buƙata, da kuma halayya ta ɗan adam. A dalilin haka wasu suka fara ɗari-ɗari da masu harkar wannan kasuwanci, saboda zarge-zargen rashin gaskiya ko rashin kyakkyawar mu’amala daga wasu ’yan kasuwar. Ko kuma yadda wasu ’yan kasuwar kan canza asalin abin da aka gani aka saya ta waya, wajen aika kayan ta tasha, da kuma matsala wajen aikawa da kayan da darajarsa ba ta kai kimar kuɗin da mutum ya biya ba.

Maryam Bichi, wata matashiyar ’yar kasuwa ce daga Jihar Kano wacce a shekaru 29 ta kasance fitacciya kuma jajirtacciya a harkar kasuwancin zamani. Bayan ƙwarewa da take da shi a kan wannan salo na neman kuɗi tana ma kuma koyar da yadda mutane za su inganta kasuwancinsu da samun karvuwa a wajen abokan hulɗarsu. Kawo yanzu wannan jarumar ’yar kasuwa ta koyar mata da matasa kimanin da dubu biyar dabarun sana’o’in zamani daban-daban.

Kuma tun a shekarar 2020 Maryam da haɗin gwiwar wasu abokan hulɗarta, ta ƙirƙiro da taron baje kolin kayan sana’o’i da wayar da kan ’yan kasuwa, wanda ta yi wa laƙabi da Taron Mu Inganta Sana’armu. Kuma sau huɗu a jere, duk shekara ’yan kasuwa maza da mata, kamfanoni, da masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i suke halartar taron da ake gudanarwa a Kano, domin baje-kolin kayayyakinsu.

A taron na wannan shekara an samu halartar ’yan kasuwa 600 daga sassa daban daban na ƙasar nan, waɗanda suka kai kayan da suke sana’antawa don ganawa da sabbin kostomomi masu sha’awa da ƙulla sabuwar alaƙar kasuwanci.

Na ɗauki dogon lokaci ina wannan bayani ne, domin nuna irin cigaban da harkar ke daɗa samu, daga kasuwanci na ɗaiɗaiku zuwa wata gamayya ko ƙawancen ƙananan ’yan kasuwa, don su ƙara haɓɓaka harkokinsu. Wani abin burgewa ma a irin wannan taro na Mu Inganta Sana’armu har taken taro ake fitarwa duk shekara, inda ake zaɓar wani batu mai muhimmanci da za a mayar da hankali a kansa, wajen faɗakar da mahalarta taron da qara wayar musu da kai, da kuma gayyatar ƙwararru da za su yi fashin baƙi a kan batun da nufin wayar da kan ‘yan kasuwa da abokan hulɗarsu. Kamar a bana, an duba yadda fasahar zamani ta kawo sauye-sauye da dama a harkar kasuwanci da cigaban rayuwa.

Ƙwararru irin su Farfesa Murtala Sagagi da Farfesa Binta Tijjani Jibrin, daga Jami’ar Bayero ta Kano, da Dr Musa Abdullahi Sufi, Aisha Othman Tofa, Alhaji Ali S. Madugu da sauransu sun faɗakar da ’yan kasuwar da kuma tunatar da su muhimmancin rungumar fasahar zamani, da cigaban kimiyya, sai kuma uwa-uba tsare gaskiya da sanya tsoron Allah a kasuwancinsu. Wannan a cewarsu shi ne zai ƙara jawo musu masu ciniki sosai, kuma ya kai sunansu inda ba su taɓa zato ba.

Hajiya Farida Musa Kalla na daga cikin ’yan kasuwar da suka kai kayansu taron baje-kolin Mu Inganta Sana’armu ta kuma ƙarfafa gwiwar mata kan muhimmancin yin kasuwanci daidai da yadda shari’a da al’adarmu ta shimfiɗa, domin hakan zai kawo ragowar matsalolin aure da zamantakewa a tsakanin iyali. Sannan ta ce, mace idan tana kasuwanci zai sa ’ya’yanta su zama a wuri ɗaya suna taimaka mata, ta yadda za a samu kyakkyawar tarbiyya a tsakanin iyalai.

Batun kasuwancin mata, musamman matan Arewa, waɗanda ita Maryam Bichi ta ce ta fi mayar da hankali a kansu, domin su ne aka fi bari a baya, ya zama wani muhimmin ɓangare da masu jawabi a taron suka ɗauki tsawon lokaci suna faɗakarwa a kai. Duba da irin yadda matsin rayuwa ya jefa iyalai da yawa cikin matsanancin hali, har ma da rabuwar aure a wasu wuraren.

Hajiya Ayah Uba Adamu wata ’yar kasuwa ce da ta shaidawa jaridar Manhaja cewa, sana’a a wannan lokacin ta zama kamar sinadarin ƙarin ingancin zaman aure ne, domin idan mace na sana’a, za ta taimaka wa mijinta ta hanyar kula da yaranta, babu ma kamar a wannan yanayin da muka tsinci kanmu na tsadar rayuwa, wanda mazan ma da suke ƙoƙarin kula da iyalansu su ma a wannan lokacin suna buƙatar tallafi daga matayensu.

Tausasa harshe, da kuma ƙarin ƙwarin gwiwa ta hanyar tallafi wajen kula da gida, a cewarta. Idan mace ba ta da sana’a duk wannan abin ba zai samu ba. Babban abinda ake so dama ya kasance a zaman aure akwai fahimtar juna, da tausayawa. Idan akwai wannan mace ko duniya ta mallaka za ta iya ba wa iyalinta, kuma wannan fahimtar juna ita za ta samar da farin ciki ga iyalinta wanda hakan zai samar da kyakkyawar al’umma.

Ita ma Aisha Adamu Sadiq matashiya kuma ’yar kasuwa cewa take yi, a gaskiya an bar yayin zaman kashe wando a wannan lokacin. Saboda ita sana’a kariya ce ga rayuwar mace, musamman wacce ta ke a matakin tasowa. Sana’a na taimaka wa wajen hana mace roƙo ko zubar da mutunci a wajen maza marasa sanin darajar mace. Kodayake da dama wasu matan babu ce ke jefa su cikin halin rashin kamun kai. Amma idan mace na da sana’a babu wata burga da wani zai yi mata. Ta ce, duk mace mai sana’a ta fi qarfin wulaƙanci.