Yadda zakin da na harba ya rikiɗe zuwa mutum – Sarkin Maharban Akko

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Alhaji Lamido Muhammad, wanda aka fi sani da Sarkin Yaƙi, shine  Shugaban Rundunar Maharba na yankin Akko a Ƙaramar Hukumar Akko da ke cikin Jihar Gombe. Shi dai Alhaji Lamido ya yi suna da tasiri, saboda irin bajitarsa da gwagwarmaya a cikin dazuzzukan Gombe, musamman dazuzzukan Akko, wurin da ya yi fice saboda ƙungurumin dazuzzuka masu cike da  dabbobi da iskokai wasu halitttun ɓoye waɗanda a cewar maharba sai ka shirya za ka iya shiga cikin su. To amma, Alhaji Lamido shi waɗannan dazuzzuka tamkar gari ne ko gida a wurin shi. ‘Na shige su sau tari, kuma na yi arangama da abubuwan ban tsaoro iri-iri, waɗansu har yau ba na mantawa da su, amma Allah ne mai kare bawa,” inji shugaban maharban, wanda a hirar shi da Manhaja a Gombe a makon jiya, ya feɗe biri har wutsiya, inda har ya tavo artabun da suka yi da`yan Boko Haram waɗanda suka kawo farmaki a garin Gombe tsakanin 2013 da 2014. Ga dai yadda hirar ta su ta kasance:
  
Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Cikakken suna na Alhaji Lamido Muhammad, amma an fi kirana Sarkin yaqi, ni ne ne kuma  shugaban duk maharban yankin Akko ta jihar, kuma yawan mambobin mu sun kai kusan mutum dubu 9,000, duk ƙwararrun maharba ne.  

A ina aka haifi Sarkin Yaƙi, kuma yaushe? 
An haife ni a wani ƙauye da ake kira Wuro-bando a Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe. Shekara ta 49, Ina da mata huɗu da ‘ya’ya 25.

Makaranta fa, wato ilmi? 
Ni dai firamare kawai na yi, sai kuma Islamiyya gwargwadon iko, Alhamdulillahi. 

Ga shi kai ne Sarkin Yaƙi, kuma shugaban maharba.To ba mu labarin yadda ka zama shugaba da kuma tarihin yadda ka zama sanannen maharbi? 
To da farko dai, ni ba kawai na zama maharbi ba ne, wannan baiwa daga  iyaye da kakanni ne. Kaka na sunan shi Baka Dikko, kuma na koyi bajintar harbi da shiga dazuzzuka daga wurin shi ba kaɗan ba.

Kenan tun ba yanzu ba ka daɗe kana gwagwarmaya a cikin daji, to ba mu labari?
(Dariya), Ka ga sana`ar mu sadaukar da rai ce, amma a wurin wasun mu, daji tamkar gida ne.  

Wato ba kwa tsoro ko fargabar shiga daji komai suƙuƙin shi?
Malam in ka ga matsoraci a daji ba ainihin marhabi ba ne, maharbin vera da gafiya ne kawai.

Amma akwai dajin da ya taɓa girgiza ka ko ya ba ka tsoro?
Ai ba kaɗan ba, amma akwai abubuwan al’ajabi biyu da suka tava ba ni tsoro a wasu ‘dajin kururuwarka banza’ da na taɓa shiga.

Me ya faru, kuma a wani daji?
Na farko shine a wani ƙungurumin daji da ake kira Zambe, a can cikin ƙarshen dazuzzukan yankin Akko, gaskiya ba kowa ne yake shiga dajin ba, amma Allah da ikon shi, na shiga, kuma na ga abin tashin hankali. Wato ina cikin lalube-lalube na a cikin wannan dajin Zambe da tsakar dare, can sai kawai na hangi wani jibgegen zaki, tsohon mafaɗacin zaki, ni dai ban taɓa ganin irin wannan zaki ba a rayuwa ta, amma haka na saita bindiga ta a kwanyar wannan zakin na harba daram. Kawai sai na ga wani hayaƙi ya tashi sama. Ni dai na tsaya inda nake ina kallon ikon Allah. Hayaƙin na tafiya, kawai sai zakin nan ya rikiɗe nan take ya zama wani ƙaton mutum, dogo sanye da baƙaƙen kaya. A nan ne fa hankalina ya tashi, sai na tuna ni fa ban zama Sarkin Marhaba haka kawai ba, kuma ni namiji ne. Kawai sai na yi maza na tura hannun dama na a cikin aljihun wando na, na damƙi wasu wasu abubuwa, na yi kuma addu`ar da na gada tun kakanni.

To me ya faru bayan nan?
Wallahi Malam dama akwai wata bishiya a can baya na, kawai sai na ganni a saman bishiyar. Sai wannan mutumin wanda zaki ne ɗazu-ɗazun nan, ya tinkaro ni har zuwa ƙarƙashin bishiyar nan da nufin ya hau. Da zuwan shi ƙarƙashin bishiyar, a sai kuwa ya sake rikiɗewa zuwa ainihin siffar shi na zaki.

To yaya ka yi a lokacin, me kuma ka ke ji?  
A lokacin sai na tuna, ni kaɗai ne fa a wannan dajin, sai Allah, sannan kuma wannan bawan Allahn (zaki). Kawai sai na yi kururuwa mai ban tsoro, na yi addua ta sahihi na saita bindiga ta a kan wannan zakin a fusace, na rinqa sake harsashi ɗaya bayan ɗaya, Ina kuma ci gaba da addua. Ai kawai in faɗa maka sai zakin ya yi likimo, sai jikin shi ya yanke ya faɗi ƙasa tim. Ni kuma na sauko na cicciɓe shi na yi gida da shi abina.

Tirƙashi! To sai me kuma bayan nan?
To sai kuma lokacin da na yi wani artabu da wani miciji ko macijiya ce,  sanin gaibu sai Allah. Domin ni ban taɓa ganin maciji mai girma da tsawo kamar wannan da na gani ba. Amma ikon Allah, ina gaban ta, na san wannan wata abin al’ajabi ce.

Yaya ka yi da ita wannan macijiya ko maciji? 
Ina ganinta tana fushi tana matsowa inda nake. Haba kawai sai na ɗirka mata harsashi. Me zan gani? Ai kuwa kawai sai ɓat ta ɓace, sama ko ƙasa. A zuciyata na ce ‘yau fa ake yin ta’, ni kuma ban matsa ko’ina ba, sai  addu’a ta nake ta yi. Can sai na ji wani irin huci, sai kawai ta ɓullo ta baya  na. Ina juyawa na sake ɗirka mata bindiga daram-daram, amma ko a jikinta, sai doso inda nake ta yi.

Ba ka gudu ba? 
In gudu in je ina? Ai da na ga bindiga da kibau ba su yi mata komai ba, sai na ajiye su a gefe na tinkare ta gaba da gaba, muka yi ta arangama  da ita. Tana ƙoƙari ta naɗe ni, ni kuma ina kaucewa. Muka yi ta bugawa, har Allah ya sa na ci ƙarfinta, ta mutu, na kwaso ta na kawo gida. To ka ji yadda muka yi da wannan macijiya ita kuma.

Lallai ka ga abun al’ajabi, sai wanne kuma? 
A nan cikin garin Gombe, ai an san irin yadda muka gwabza da yan Boko Haram a wuraren shekarar 2013 ko 2014, lokacin da suka kawo hari nan garin. Ai mun tarwatsa su ga jamian tsaro. Ai a locakin, har Gwamna Ɗankwabo ya yaba mana.

To irin gudunmuwar da kuke bayarwa na tsaro, kun tava samun wani tallafi daga hukuma?
Mu muna sa kai ne da tallafa wa al’umma don a samu zaman lafiya. Amma ba mu taɓa samun wani tallafi ba, sai dai kuma Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi mana alƙawari zai taimaka mana, don  mu masu goyon bayan shi ne, kuma muna roƙon shi da ya cika alƙawarin da ya yi mana, musamman kayayyakin aiki kamar babura, motocin fatirin da makamantansu, saboda shiga lunguna da saƙuna na jihar mu don magance kowace irin barazana ce daga miyagu. A yanzu mu ne muke ɗaukar nauyin duk abubuwan da muka tsara yi.

Yaya alaƙar ku da jami’an tsaro a jihar?
Alhamdulillahi, muna da kyakkyawar dangantaka da su, babu matsala, musamman DPO na yankinmu, yana ba mu haɗin kai sosai

Ko akwai wani qarin bayani da ka ke son yi? 
To ƙarin bayani dai, shi ne gwamnati ta tallafa mana saboda aikin mu, aikin haɗari ne, amma muna iyakar ƙoƙarin mu wajen bada tsaro a duk faɗin jihar mu ta Gombe. Wani abu kuma shine, ina jan hankalin jama`a da su lura da wasu masu ƙaryar cewa su maharba ne, suna karɓar kuɗi daga hannun su da sunan za su ɗauke su aikin tsaro na maharba. Masu sha’awar aikinmu, su garzayo ofishinmu a kasuwar Gwari, Tumfure kawai su yi rajista.

Mun gode.
Ni ma na gode.