Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rashin jituwa da ake zargi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da gwamna mai ci a Kaduna, Sanata Uba Sani ya fito fili, bayan tsohon gwamna ya yi kakausan martani kan kalaman gwamna mai ci.
Wannan sabuwar taƙaddama da ta kunno kai na da nasaba da kalaman da gwamna Uba Sani ya furta a lokacin wata hira da kafar talabijin ta TɓC a Nijeriya, wadda ba ta yi wa tsohon gwamna El-Rufa’i daɗi ba.
Mutanen biyu waɗanda a baya aminan juna ne a fagen siyasa, abubuwa sun sauya tun bayan sauyin gwamnati da kuma takun-saƙa da ta kunno kai bayan da Uba Sani ya hau kan kujerar gwamna.
Daga lokacin ne aka fara bijiro da batun binciken gwamnatin El-Rufa’i kan yadda gwamnatinsa ta kashe kuɗi a zamaninta.
Masana siyasa na ganin cewa ba sabon abu ba ne a samu ɓaraka tsakanin tsohon gwamna da magajinsa a Nijeriya, kamar yadda aka gani a jihohi da dama.
A wata hira ta musamman da gidan talabijin na TɓC an yi wa Uba Sani tambaya kan mene ne ra’ayinsa kan batun masu neman yin haɗaka domin kifar da gwamnatin Tinubu.
Wajen mayar da martani gwamna Uba Sani ya ce “zance na gaskiya shi ne, wasu mutane,” ciki har da magabacinsa “na fitowa suna suka kan abubuwan da ba gaskiya ba”.
Kuma a cewarsa waɗannan masu sukar mutane ba sa ɗaukar su da wani muhimmanci saboda sun fahimci duk wannan fafutikar ta kashin-kai ce ba wai tausayin al’umma ba.
Sannan ya ce, “Ya za a yi gwamnatin da ba ta yi shekara biyu ba, a ce mutanen da suka rasa gwamnati su za su fito suna suka.
“Ai galibinsu sun yi mulkin shekara takwas kuma ba a ga wani abu na arziki ko rawar ganin da suka taka ba.”
Waɗannan kalamai da Uba Sani ya ke yi tamkar gugar-zana ce ga magabacinsa Malam Nasir El-Rufa’i.
Saboda ya cigaba da cewa, “sanin kowa ne cewa ai jam’iyyarmu ɗaya, sun ba ni mamaki kuma na kaɗu da abubuwan da suke yaɗawa.”
Gwamna Uba Sani ya ce idan aka bincika “me suka yi wajen tabbatuwar dimokuraɗiyya da mulki na adalci da jin-ƙai, babu abin yabawa.
“Mutanen da ke ta bibiyar Tinubu ne a baya, amma saboda sun rasa samun shiga ko dama sai a koma suka.
“Dukkaninsu babu mutum ko guda da ya kwatanta dimokuraɗiyya da sanin dimokuraɗiyya fiye da Tinubu don haka kawai shaci-faɗinsu ne.
“Ai tare muke zama muna rayuwa da galibinsu, kuma su ma a wannan lokacin sun yi amanna cewa babu wanda ya cancanci wannan ƙasa sama da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Don haka a yanzu mene ne ya sauya? Kawai suna waɗannan kalamai ne da bakin adawa saboda ba su samu abubuwan da suka yi tunani a mulkin ba, ko sun rasa gwamnati.”
Duk da dai gwamnan Uba Sani ya nuna cewa yana waɗannan maganganu ne ba wai a matsayin ɗan siyasa ba, amma a matsayin ɗan kishin ƙasa, tsohon gwamna El-Rufai ya mayar masa da martani.
A shafinsa na ɗ, El-Rufa’i ya tabbatar da cewa ba sa jituwa da Uba Sani, saboda ya rubuta cewa, “a duk lokacin da na ga wannan gwamna ya fito yana ɓaɓatu da baza rashin basira da abin kunya, sai na shiga mamaki ya aka yi haka.
“Amma babu komai kuma wannan tayar da jijiyoyin wuya da Uba Sani ke yi saboda kuɗaɗen da gwamnatin Tinubu ta bai wa Kaduna na naira biliyan 150 a cikin watanni 18 ne, sai a fito a yi bayyani yadda aka yi da kuɗaɗen.
“An dage ana kare Asiwaju saboda kuɗaɗen da aka samu, Asiwaju ya ci riba, a kanka. Mutanen Kaduna za su yi hukunci a lokacin da ya dace a inda kuma ya dace.”
Wanna martani da tsohon gwamnan ya mayar da ya ja hankalin al’umma tare da haifar da muhawara a shafukan sada zumunta.
Duk da cewa an daɗe ana raɗe-raɗi kan alaƙar mutanen biyu, abin da ya fito fili shi ne lokacin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta ƙaddamar da binciken kan tsohon gwamna El-Rufai bayan an zarge shi da karkatar da naira biliyan 432 a shekaru takwas na mulkinsa.
Tun daga wancan lokaci ake ci gaba da tuhumar wasu jami’an tsohuwar gwamnatin kan zargin rashawa.