Yahaya ya miƙa saƙon goron sallah ga sojoji da iyalansu

Daga AISHA ASAS

Shugaban Sojojin Nijeriya, Lieutenant General Farouk Yahaya, ya miƙa saƙon taya murnar bikin Babbar Sallah ga sojojin Nijeriya da iyalansu.

Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Yahaya ya ce, “Ina farin cikin taya ɗaukacin sojojin Nijeriya da iyalansu murnar bikin Babbar Sallar 2021.”

Ya ce bikin Babbar Sallah lokaci ne da ke tunatar da al’umma game da biyayya da sadaukarwa wanda hakan na daga cikin kyawawan ɗabi’un kowane nagartaccen soja. Tare da yin godiya ga Allah Maɗaukaki bisa rahmarSa da kariyarSa a kansu yayin da suke ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a kansuna na yi wa ƙasa aiki.

Don haka ya ce bikin Idul Kabir lokaci ne da ke ba su dama ta musamman da kuma ninka ƙoƙarinsu wajen sauke nauyin da dokar ƙasa ta ɗora musu na bai wa ƙasa kariya da kuma daƙile harkokin tada-zaune-tsaye.

A cewarsa, “Ko shakka babbu ƙasarmu na fuskantar matsalolin tsaro. Kuma gwargwadon hali sojojin Nijeriya sun yi abin da ya kamace su kuma za su ci gaba jajircewa wajen yaƙi da waɗannan matsaloli.”

Daga nan jami’in ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa da kuma jinjina wa rundunonin Operation HADIN KAI da HADARIN DAJI da THUNDER STRIKE da WHIRL STROKE da dai sauransu, waɗanda ke aiki ba dare ba rana wajen ba da gudunmawarsu a gida da ƙetare.

Ya ci gaba da cewa tun bayan da ya ɗare kan sabon muƙaminsa ya yi alƙawarin kyautata wa sojojin Nijeriya ta fannoni daban-daban, wanda ta dalilin haka ne ma aka bai wa wasu jami’ai da suka cancanta lambobin yabo yayin taron NADCEL da aka gudanar a ranar 6 ga Yulin 2021.

Yana mai cewa wannan somin taɓe ne, domin kuwa haka zai ci gaba da yaba wa dukkan jami’an da suka cancanci a yaba musu don ƙara musu ƙwarin gwiwa.

A ƙarshe, Yahaya ya yi godiya ta musamman ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa irin goyon bayan da yake bai wa sojojin Najeriya domin ƙarfafa musu wajen gudanar da harkokinsu yadda suka dace.