Yajin aiki: ASUU ta ce za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu

Biyo bayan umarnin da kotu ta bai wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) kan mambobinta su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba, ƙungiyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa kotu ta gaba.

A ranar Laraba ce dai Kotun Ma’aikata ta Kasa ta bai wa malaman jami’o’in umarnin komawa bakin aiki har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar.

Amma ASUU ta ce ta soma hada kan jiga-jigan lauyoyi karkashin jagoranci babban lauyan nan, Femi Falana don su wakilce ta wajen daukaka karar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ran Laraba, shugaban ASUU na shiyyar Legas, Adelaja Odukoya, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu sannan su hada kai su ci gaba da wannan gwagwarmayar har zuwa karshe.

Tun farko, an rawaito Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke na cewa, za su zauna su tattauna kan umarnin da kotu ta ba su na su koma bakin aiki.

Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta soma wannan yajin aikin ne ran 14 ga Fabrairun da ya gabata da zummar neman hakkokinta a wajen Gwamnatin Tarayya.