Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NARD) ta ƙi amincewa da ƙarin kashi 25 na albashi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi don inganta albashin likitoci.
Ƙungiyar ta ɗauki matakin ƙin amincewar ne a wajen taron shugabanninta na ƙasa (NEC) da ya gudana a Legas, inda ta fitar da bayanin sakamakon taro a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Orji Emeka Innocent da sakatarenta na ƙasa, Chikezie Kelechi da kuma Umar Musa.
Likitocin sun dage kan cimma ainihin buƙatunsu da suka haɗa da cikakken aiwatar da tsarin albashi na CMSS da aka amince da shi tun a 2009.
Don haka likitocin suka ce ba zai yiwu su amince da ƙarin kashi 25 na albashin da Shugaba Tinubu ya yi musu tayi ba har sai gwamnati ta yi abin da ya kamata
A cewar sanarwar, “NEC ba ta amince da ƙarin kashi 25 a albashi da alawus ɗin likitoci ba. Cikakken aiwatar da tsarin albashi na CSMSS muke buƙata wanda aka amince da shi a 2009.”