Yajin Aiki: Gwamnati ta roƙi likitoci da su koma bakin aiki don ceton rayuka

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta roƙi Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD) a kan ta dakatar da yajin aikin da mambobinta ke yi don ceto rayukan marasa lafiya da ke kwance a asibitocin faɗin ƙasar.

Babbar Sakatatiyar Ma’aikatar Ƙwadago da Bada Aiki, Mrs Daju Kachallom ce ta yi wannan roƙo sa’ilin da take zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ta ce likitocin su dubi Allah su dubi Annabi, ka da su bari a ci gaba da samun asarar rayukan ‘yan Nijeriya a asibitoci saboda rashin samun kulawa.

Kachallom ta bai wa likitocin tabbatacin Gwamnatin Tarayya na yin dukkan mai yiwuwa domin cim ma buƙatunsu cikin ƙanƙanin lokaci.

Ta ƙara da ccewa, akwai buƙata kwamitin da NARD ta kafa ya kammala aikinsa cikin lokaci domin bai wa gwamnati damar aiwatar da shawarwarin da zai bayar a kan kari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *