Yajin aiki: Muna nan kan bakanmu – SSANU/NASU

Daga AISHA ASAS

Haɗaɗɗen Kwamitin Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASU) da kuma Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i (SSANU), ya tsayar da ranar Juma’a (05/02/2021) a matsayin ranar da mambobin ƙungiyoyin biyu za su soma yajin aiki na sai baba-ta-gani sakamakon gazawar da suka ce gwamnati ta yi wajen biya musu buƙatunsu.

Tun farko, sai da ƙungiyoyin suka bai wa gwamnati wa’adin makonni kan ta magance musu matsalolinsu ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Shugaban SSANU Muhammed Haruna, ya shaida wa Manhaja cewa, babu wata yarjejeniya da ƙungiyoyin suka cim ma da gwamnati kan janye ƙudirin shiga yajin aikin.

Yana mai cewa, tattaunawar da haɗaɗɗen kwamitin ƙungiyoyin zai yi a wannan Juma’a game da roƙon da Gwamnatin Tarayya ta yi, ita ce za ta nuna jayen aniyar shiga yajin aikin ko kuwa a’a.

Sai dai sugabannin ɓangarorin biyu sun ce babu ja da baya za su soma yajin aikin nasu da ƙarfe 12 na dare na wannan Juma’a.

Ƙungiyoyin sun ce, ganawar da suka yi da Ministan Ƙwadago, Dr Chris Ngige domin dakatar da shirin shiga yajin aikin, ba ta haifar da ɗa mai ido ba.

Daga cikin buƙatun ƙungiyoyin har da neman a biya su bashin ariyas na mafi ƙarancin albashi da batun tsarin biyan albashi na bai ɗaya (IPPIS), da rashin biyan alawus da jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da suka cim ma da gwamnati a 2009, da dai sauransu.