Yajin aikin ASUU: Ɗaliban Nijeriya sun bada wa’adin kwanaki tara a buɗe jami’o’in gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS reshen Kudu maso Gabas ta bai wa Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU wa’adin kwanaki tara da a buɗe dukkanin jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasar.

Shugaban NANS na shiyyar F, Kudu Moses Onyia, ne ya bada wa’adin a cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa kan harkokin yaɗa labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

Idan za a iya tunawa, ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargaɗi na watanni uku da wasu watanni uku.

Sanarwar ta ce ya kamata gwamnati da ASUU su yi abin da ake buƙata kafin kwana tara, ta ƙara da cewa rashin yin hakan a cikin ko kuma a ƙarshen wa’adin zai bar ɗalibai da matakin ƙarshe na ɗaukar wani mataki mai tsauri.

A cewar sanarwar, “daga ranar 20 zuwa 25 ga Mayu, 2022; bayan ƙarewar wa’adin, za mu ɗauki matakan da za su ga ɗaliban Nijeriya na shiyyar Kudu maso Gabas a adadinsu sun toshe ɗaya daga cikin manyan hanyoyin shiga Kudu maso Gabas zuwa Gadar Neja.

Ya ce: “Za kuma mu toshe dukkan filayen jiragen sama guda uku da ke Kudu maso Gabas, waɗanda suka haɗa da: filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu; Sam Mbakwe Airport, Owerri da Anambara Passenger and Cargo International Airport, Umeri, Anambara.

“Don haka, dakatar da duk wani motsi zuwa ko daga waɗannan kusurwoyi na Kudu maso Gabas,” inji shi.