Yajin aikin ASUU: Jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya suna ta samun ƙarin ɗalibai

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya sun ƙara tumbatsa sakamakon ɗalibai da suke rigegeniyar shiga sakamakon rufe jami’o’in gwamnati da aka yi sanadiyyar yajin aikin ASUU.

Idan za a iya tunawa, tun 14 ga watan Fabrairu, 2022 ne aka tsayar da duk wata hada-hada ta koyarwa ko koyo a jami’o’in Nijeriya mallakar gwamnati saboda yajin aikin da ƙungiyar Malamai da ma’aikatan jami’o’i (ASUU) suka tsunduma.

Ƙungiyar tana neman kuɗaɗen inganta jami’o’in ne daga wajen gwamnati na yarjejeniyar 2009 FGN/ASUU da alawus-alawus na malaman da ya maƙale da kuma tabbatar da adalci a wajen harkar kuɗi a jami’o’in.

Makwanni biyu da suka wuce, Ministan ma’aikatar ilimi mai zurfi, Adamu Adamu ya bayyana cewa, gwamnatin Tarayya ta riga ta biya wa ƙungiyar mafi yawa daga buƙatunta da suke nema daga gwamnati, waɗanda suka ƙunshi Naira biliyan 50 na alawus-alawus ɗin malaman Jami’o’i da ma’aikatunta.

Amma a cewar sa, gwamnati ba za ta ɗauki nauyin biyan ASUU albashin tsahon lokacin da suka ɗauka suna zaman yajin aiki ba.

Sai dai kuma su ma ƙungiyar ASUU sun ja tunga sun ƙeƙasa ƙasa a kan ba za su koma bakin aiki ba har sai an biya su waɗancan bashin albashi da suke bi.

Wannan alamu da suke nuna wannan yakin aiki wanda ya cika kwanaki 200 cif a ranar biyu ga watan Satumba ba shi da ranar ƙarewa.

Sai dai kuma da yake faɗuwar wani, wani lokacin kan zama tashin wani, jami’o’i masu zaman kansu da suke a johohin Kano, Kaduna, da Katsina sun bayyana cewa, su yajin aikin ASUU gaba ta kai su.

Domin su sun ci riba da shi. Sai dai a cewar su, yajin aiki ba abin farin ciki ba ne, saboda koma-bayan da yake kawowa a fannin ilimi.

Wata majiya daga jihar Kano ta bayyana cewa, wannan yajin aikin wanda ya haura watanni shida ya taimaka sosai wajen ƙara samun ɗalibai a jami’o’i biyar masu zaman kansu da suke a jihar.

Jami’o’in su ne, Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN), Jamiar Skyline, Kano, Jami’ar Al-Istiqama, Sumaila, sai jami’ar Baba Ahmed.

A ta bakin mai magana da yawun jami’ar MAAUN, Tukur Masanawa, a juyin da aka dawo na sabon zangon karatu na 2021/2022, jami’ar ta ɗauki ɗalibai fiye da 1,000.

Hakazalika, shi ma mamallakin jami’ar Al-Istiqama, Abdurrahman kawu Sumaila, ya bayyana cewa, jami’ar ta samu ɗalibai masu yawa sakamakon yajin aikin.

A cewar sa ma, banda sabbin ɗalibai akwai wasu masu ɗimbin yawa da suka fita daga jami’o’in gwamnati suka shigo don cigaba da karatunsu a jami’ar.