Yajin aikin ASUU: Za mu rufe filayen jirage, titina da wajen zaɓukan fidda-gwani – NANS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), ta yi barazanar rufe filayen jirgin sama, manyan tituna da guraren zaɓukan fidda-gwani a ƙasar nan domin nuna rashin jin daɗin ta da ƙarin tsawaita yajin aiki da ASUU ta yi na makonni 12.

A wata sanarwa da Shugaban NANS na Ƙasa, Sunday Asefon ya yi a ranar Litinin, ƙungiyar ta yi alla wadai da abinda ta suffanta da halin ko-in-kula da Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke yi a kan lamarin.

Shugaban NANS ɗin ya kuma tabbatar da cewa ɗalibai za su yi tsinke a duk guraren zaɓukan fidda-gwani da taruka da jam’iyyu za su yi a ƙarshen watan Mayu.

A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya suka shiga yajin aikin jan kunne domin assasa biyan wasu buƙatunsu daga Gwamnatin Tarayya, lamarin da ya yi ƙamari tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, babu biyan buƙata ba kuma komawa makarantu.

Malaman jami’o’in sun buƙaci gwamnati da ta tabbatar da yarjejeniyar da suka saka hannu a watan Disamban 2020 kan kuɗin da za a fitar wurin farfaɗo da jami’o’in gwamnati.

Sauran buƙatun malaman sun haɗa da biyansu alawus ɗin su, sake sasantawa kan yarjejeniyar 2009 da kuma amfani da tsarin biyan albashi da fasahar UTAS da sauransu.

A ɗaya ɓangaren, Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin yi, Dr. Chris Ngige, a ranar Juma’a ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya da ASUU za su cigaba da tattaunawa a cikin makon nan.