Yajin aikin gargaɗi: NLC ta ƙaurace wa zaman sulhu da Gwamnatin Tarayya

Shugabanni ƙwagiyar ƙwadagobta ƙasa (NLC) sun ƙaurace wa taron Ministan Ƙwadago, Simon Lalong, da zummar daƙile yajin aikin gargadi na yini biyun da ƙungiyar ta ƙuduri aniyar farawa.

Majiyarmu ta shugabannin ƙungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ne kaɗai aka gani a wajen taron wanda aka fara da misalin ƙarfe 5:52 na yammacin ranar Litinin.

A ranar Juma’a NLC ta bayyana aniyyarta ta fara yajin aiki na kwana biyu a faɗin ƙasa daga ranar Talata, 5 ga Satumba, a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayya.

NLC ta ce ta ɗauki matakin yin yajin aikin ne domin nuna wa duniya rashin jin daɗinta dangane da ƙuncin rayuwar da ta ce ‘yan ƙasa na fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *